Shugaban Karamar Hukumar Ungogo a Jihar Kano, Abdullahi Garba Ramat, ya ajiye kujerarsa, a yayin da na karamar hukumar Nassarawa ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar.
Honorabul Abbdullahi ya ajiye kujerar ne a wani kwarya-kwayan taron rabon kayan tallafi ga mata 500, da kuma bude ofisinsa; kwanaki kadan bayan cikar wa’adinsa da ya fara a watan Maris, 2021.
Sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Litinin, ya ce, “Alhamdullah, yau an mika ragamar shugabancin Karamar Hukumar Ungogo ga mataimakina. Na yi iya kokarina, inda na samar da abubuwan more rayuwa, har majalisar dokokin jiha ta ayyana a matsayin gwarzon shugaban karamar hukuma.”
A gefe guda kuma, Shugaban Karamar Hukumar Nassarawa ta Jihar Kano, Auwalu Lawan Shaaibu wanda aka fi sani da Aranposu ya sauya sheka daga Jam’iyyar APC zuwa NNPP mai mulkin jihar.
- Zan hade Kannywood da Nollywood —Ali Nuhu
- Kungiyoyin Arewa sun caccaki masu sukan tsare-tsaren Tinubu
A safiyar Talaa ya sanar da sauya shekarsa a Facebook da cewa, “Na dawo gidana… Gwamna Abba Kabir Yusuf masoyin Kano da al’umma ne, mu ci gaba da yi masa addu’a.”
Hadimin gwamnan kan kafofin sada zumunta Salisu Yahaya Hotoro ne ya fara dora hoton Aramposu tare da da Gwamna Abba, kowannensu sanye da jar hula.
Wakilinmu ya so samun karin bayani kan lamarin daga gare shi, amma haka bai samu ba, saboda wayarsa ba ta shiga, kuma ba mu samu amsar rubutaccen sakon da aka aika masa ba, har muka kammala rubuta wannan labarin.