✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan hade Kannywood da Nollywood —Ali Nuhu

Ya yi alkawarin farfado da kasuwar fina-finan Kannywood da kuma hade su da Nollywood domin samun cigaba da ake bukata

Shugaban Hukumar Fina-finai Ali Nuhu vows ta Kasa, Ali Nuhu, ya yi alkawarin habaka kasuwar fina-finan Kannywood ta yadda za farfado daga halin da take ciki.

Ali  Nuhu ya yi alkawarin bunkasa Kannywood ta hanyar ba wa ’ya’yanta horo da kwarewar da za ta yi gogayya da takwararta ta Nollywood da ke kudancin Najeriya.

“A kashin farko na abubuwan da za mu yi a bangaren Kannywood, akwai ba da horo, da sake bude kasuwar fina-finan wanda yanzu shi ne babbar matsalar masana’antar. Daga Kannywood nake, saboda haka na san abin da ke ci mana tuwo a kwarya,” in ji shi a wurin taron liyafar da ’yan Kannywood ta shirya a Kano domin taya shi murnar samun mukamin.

Shugaban hukumar ya ci gaba da cewa, shiryen-shiryen da ya tsara a hukumar za su kawo ci gaba ba ga Kannywood kadai ba, har ma ga daukacin masana’antar fim din Najeriya.

“Za mu tattauna mu duba bangarorin da aka bar mu a baya a tsawon shekaru ba Kannywood kadai ba, a’a masana’antar fim din kasar nan gaba daya za mu duba, domin ganin hadewarta a wuri guda cikin hadin kai da kuma aiki tare.”

Ali Nuhu wanda shi ne dan Arewa na farko da ya zama Manajan Daraktan Hukumar Shirya Fina-finai ta Kasa, ya ce zai yi iya bakin kokarinsa, wajen sauke nauyin da aka dora masa, domin ba wa marada kunya.