Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta ce ta yanke shawarar dasa kyamarorin da za su rika samar da bayanan yadda al’amurra ke gudana (CCTb) a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano a duk lokacin da wasa ke gudana don gudanar da cikakken tsaro.
Mahukuntan kulob din sun ce sun yanke shawarar yin haka ne bayan hargitsin da ya faru a filin a makon jiya a lokacin da magoya bayan kulob din suka lakadawa direban motar kulob din Enyimba duka sabili da rashin nasara da kulob din ya samu a wajen Enyimba a gasar rukuni-rukuni na Najeriya.
Jim kadan bayan Enyimba ta samu nasara a kan na Pillars da ci 2-1 ne a filin wasa na Sani Abacha, sai magoya bayan Pillars suka shiga yin bore don nuna bacin ransu al’amarin da ya sa suka yi wa direban Enyimba dukan kawo wuka. Su kansu ’yan kwallon Enyimba sai da suka nemi mafaka a wurin jami’an tsaro kafin su tsira daga fushin magoya bayan na Pillars.
Wannan ta sa aka rika hasashen Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya NFF ta hannun kwamitin da ke lura da yadda gasar ke gudana (LMC) za ta ci tarar Pillars kuma akwai yiwuwar a dage kulob din daga yin wasansa na gida a Kano zuwa wata jiha.
Sai dai kafin daukar wannan mataki ne mahukunta kulob din suka fitar da sanarwar yanke shawarar dasa kyamarori a lunguna da kuma sakon filin wasa na Sani Abacha don kaucewa sake faruwar irin haka nan gaba.
Ana ganin, wannan mataki da Pillars ta dauka abu ne da ya dace kuma akwai yiwuwar kwamitin lura da gasar (LMC) ya sassauta wa kulob din wajen zartar masa da hukunci.
Su dai magoya bayan Pillars an shaide su da yawan tayar da rikici a duk lokacin da kulob din ya samu rashin nasara a lokacin da yake yin wasa a gida. An sha dage kulob din daga yin wasanninsa na gida zuwa wasu jihohi saboda yadda magoya bayan kulob din suke nuna rashin halin dattaku.
Kano Pillars za ta dasa kyamarori a filin wasa na Sani Abacha
Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta ce ta yanke shawarar dasa kyamarorin da za su rika samar da bayanan yadda al’amurra ke…