✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano Pillars ta samu sababbin ’yan kwallo 8

Kimanin ’yan kwallo takwas ne suka samu nasarar komawa kulob din Kano Pillars.Daga cikin ’yan kwallon akwai hudu daga kulob din Giwa FC da ke…

Kimanin ’yan kwallo takwas ne suka samu nasarar komawa kulob din Kano Pillars.
Daga cikin ’yan kwallon akwai hudu daga kulob din Giwa FC da ke Jos watau Charles Henking da Dadung Amos Gyang da Chris Madaki da kuma Olorunkeke Ojo.
Sauran ’yan kwallon da suka koma kulob din na Pillars sun hada da Ifeanyi Nweke daga Nasarawa United da King Osunga daga Warri Wolbes da Razak Adegbite daga Sunshine Stars da kuma Emmanuel Ambrose daga Kaduna United.
Idan za a tuna, kwamitin ladabtarwa na Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ya dakatar da kulob din Giwa FC daga gasar rukunin firimiya bayan an same shi da laifin kin halartar wasanni uku.  Hakan ta sa ’yan kwallon suka bazama don canza sheka zuwa wasu kulob don cigaba da kwallo.