✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano: Nan gaba za a yanke hukuncin karar da Sarki Aminu ya shigar

Sarki Aminu ya je gaban Babbar Kotun Tarayyar da ke zamanta a Kano inda ya nemi ta hana Gwamnatin Kano da jamian tsaro kama shi.

Kotu fara sauraren karar da Sarki Aminu Ado Bayero ya shigar na neman hakkinsa na dan Adam wanda ya ce Gwamnatin Kano ta take masa.

Sarki Aminu ya je gaban Babbar Kotun Tarayyar da ke zamanta a Kano inda ya nemi ta hana Gwamnatin Kano da jamian tsaro kama shi.

Wadanda ake kara sun hada da Kwamishinan Shari’a da Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano da Kwamishinan ’Yan sanda da shugaban ’yan sanda da sauransu.

Lauyan wanda ake kara Mahmud Magaji (SAN) ya nemi kotu ta soke umarnin da ta fara bayarwa na kama shi da kuma yi masa barazana duba da cewa kotun ba ta da hurumin sauraren shari’ar.

Barista Magaji ya shaida wa kotun cewa mai kara ya shigar da kara kwana biyar bayan an sauke shi.

“Idan har hakan ta tabbata to mai kara ya shigar da karar ne a lokacin da ba ya kan kujerar Sarki, don haka ba shi da kowane irin hakki da zai nema”

Haka kuma ya shaida wa kotun cewa “kasancewa sarki ba hakki ba ne, dama ce”

Lauyan mai kara Michael Jonathan Numa (SAN) ya bayyana wa kotun cewa kotun tana da hurumin sauraren shari’ar duba da cewa Majalisar Kasa tana da doka cewa Gwamnatin Tarayya tana da dama a kan duk wani sha’anin da ya shafi jihohi.

Ya kuma shaida wa kotun cewa lokacin da aka ce an cire mai kara ba a ba shi damar sauraren sa ba haka kuma ba a bi hanyar da ta dace wajen sanar da shi batun cire shi ba, domin ya tsinci maganar ne a kafafen sada zumunta, wanda hakan keta hakkinsa ne a matsayinsa na dan Adam.

Barista Jonathan ya shaida wa kotun cewa sun janye rokonsu guda biyu da ke gaban kotun .

Alkalin kotun, Mai Shari’a Justis Simon Amobeda ya ce za a sanar da ranar da kotun za ta yanke hukunci a kan wannan mas’ala anan gaba’.