✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shari’ar Kano: Lauyoyin Arewa 200 sun lashi takobin taimakon Abba a Kotun Koli

Lauyoyin sun bukaci a bar bangaren shari'a ya yi aiki da doka da oda don tabbatar da adalci.

Lauyoyin sa-kai kimanin 200 daga jihohin Arewa 19 suka kudiri aniyar taimaka wa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano domin samun nasara a  karar da ya daukaka zuwa Kotun Kolin kan shari’ar zaben jihar.

Lauyoyin sun bayyana haka ne a ranar Lahadi a lokacin da suke tattaunawa da manema labarai a Kaduna a karkashi kungiyar ‘Abba Kabir Yusuf Volunteer Lawyers Forum For The 19 – Northern States And Abuja’.

Mai magana da yawunsu lauyoyin, Yusuf Ibrahim, ya bayyana goyon bayansu ga Abba ya kuma bayyana cewa hukuncin kotun daukaka kara ta yanke na tabbatar wa da APC nasara rashin adalci ne.

“A matsayin masu aikin shari’a masu zaman kansu za mu tsaya don shiga cikin shari’ar hadin kai ga Gwamna Yusuf a Kotun Koli ta Najeriya.

Ibrahim ya kara da cewa “Muna so mu wakilci gaskiya a yakin kwato masa mulkinsa da na al’ummar Jihar Kano.”

Lauyoyin sun bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da Kotun Koli kada su bari a yi wa dimokuradiyya kisan mummuke a Najeriya ko mayar da kasar mai tsarin jam’iyya daya.

Sun kuma yi kira ga kotun kolin da ta bijirewa duk wani katsa-landan daga wasu domin kare martabar bangaren shari’a da kuma tabbatar da doka da oda.

Da suke nuna damuwarsu kan ’yancin cin gashin kai game da bangaren shari’a a Najeriya, kungiyar lauyoyin ta ce, dole ne a bi doka don tabbatar da kuri’un kowane dan Najeriya a lokacin zabe.

Kungiyar ta kuma bukaci a sake yin aiki da dokar zabe.