✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kano: Gamayyar kungiyoyin Tijjaniya sun bukaci a zabi Abba Gida-Gida 

Sun ce ba da yawunsu wasu suka nemi a zabi wani dan takara ba

Gamayyar Kungiyoyin Darikar Tijjaniyya ta nesanta kanta daga wata sanarwa da wasu da ta ce sun fake da darikar suna kira da a zabi wani dan takarar Gwamna a Jihar Kano.

Kungiyoyin sun bayyana haka ne a wani taron manema labarai da suka gudanar a cibiyar ’yan jarida ta Kano karkashin jagorancin Sheik Tijjani Sheik Sani Auwal, Shugaban kungiyar Majma’u Ahbabu Sheik Ibrahim Inyass ta kasa kuma shugaban ” TIGMEN.

Ya yi kira ga ga mabiya darikar da su fito mazansu da mata a ranar Asabar su zabi dan takarar jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf a matsayin Gwamnan Jihar Kano.

Shugaban ya ce sun yanke hukuncin ne la’akari da cancanta da dacewarsa da kuma makomar al’ummar Jihar.

Sheikh Tijjani, wanda jikan Shehu Ibrahim Inyass ne kuma mai magana da yawun Shehu Mahi, Halifan na Inyass a Najeriya ya jaddada barranta kansu daga duk wasu masu fakewa da sunan darikar, suna ba da sanarwar a zabi wani dan takara da sunansu.

A yayin taron ’yan jaridaR, Sheik Tijjani yana tare da wakilcin kungiyoyi da mukaddamai ya ce sun yarda a zabi Abba Gida-Gida ne saboda yarda da ingancinsa da kuma imaninsu cewa zai kuma ba da gudummuwa wajen ci gaban ilimi da sauran fannoni na ci gaban rayuwa.