Gwamnatin Kano ta ba da umarnin bude makarantun kwanan da ta rufe a farkon shekarar nan a jihar saboda matsalar tsaro.
Hakan na kunshe ne a cikin umarnin da ta bayar komawa makarantu a ranar Litinin 17 ga Mayun 2021, bayan kammala hutun Karamar Sallah.
- Kurunkus: Sunusi II ya zama Halifan Tijjaniyya a Najeriya
- An kara kona ofishin ’yan sanda a Abiya
- Shugabannin Tsaro na ganawar sirri da Majalisar Tarayya
- Bikin Sallah: An dakatar da kilisa da hawan Sallah a jihar Neja
Kwamishinan Ilimin Jihar, Muhammad Sanusi-Kiru, ta hannun kakakin Ma’aikatar, Aliyu Yusif, ya ce “Ana umartar daliban makarantun kwana su koma makaranta a ranar 16 ga Mayu, 2021, makarantun je-ka-ka-dawo kuma 17 ga Mayu, 2021.
“Gwamnati na kokarin tabbatar da ganin yara sun samu ingantaccen ilimi; don haka ana bukatar iyaye da su mayar da ’ya’yansu makarantu a kan lokaci,” inji sanarwar.