Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya umarci masu yin gine-gine a filayen da Gwamnatin Ganduje ta sayar musu a sansanin alhazan jihar da su dakata, nan take.
Gwamnan ya ba da umarnin ne a ranar Juma’a bayan da ya kai ziyarar gani da ido zuwa sansanin alhazan. A ranar ce kuma gwamnatinsa ta fara rushe wasu gine-gine da aka yi ba bisa ka’ida ba a Filin Sukuwa da ke garin Kano.
“Na yi takaicin ganin yadda gwamnatin da ta shude ta mayar da sansanin alhazan Jihar Kano, inda ta sayar wa ’yan koronta da filayen sansanin.
“Saboda haka na umarci duk masu yin gine-gine a sansanin alhazai da su dakat nan take, a yayin da muke ci gaba da daukar matakan ingancin sansanin alhazan domin walwalan maniyyatan Jihar Kano na wannan shekarar,” kamar yadda gwamnan ya wallafa a shafinsa na Twitter.
- Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 80, wasu 876 Sun Mika Wuya A Borno
- Yadda aka sayar wa maniyyatan Kano kujerun Hajji na bogi
Hakan kuwa na zuwa ne washegarin da sabon Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai na jihar, Rabi’u Danbappa ya zargin magabacinsa da sayar wa maniyyata kujerun Hajji 190 na bogi.
A lokacin da yake karbar jagorancin hukumar a hannun tsohon shugabanta, Muhammad Abba Danbatta a ranar Alhamis, ya ce, “Na tarar sun sayar da kujeru fiye da wadanda Hukumar Aikin Hajji a Kasa (NAHCON) ta ba jihar.
“A ka’ida Hukumar NAHCON ta ba Jihar Kano kujeru 6,082, amma sai suka sayar da 6,273; Ba ka da abu, bai kamata ka sayar da abin da ba ka da shi ba. Wannan kuskure ne,” in ji shi.
A cewarsa, ya yi kokarin neman karin kujeru, amma Hukumar NAHCON ta shaida masa cewa ba ta da wasu kujeru da za ta iya kara wa jihar.
Ya ce, saboda haka sai da maniyyatan da hakan ya ritsa da su “su nemi tsohon shugaban Hukumar don neman kudadensu.”
Danbappa wanda ya taba jagorancin hukumar sau biyu, ya ce, “Ni duk tsawon zamana a wannan hukumar ban taba sayar da kujerun da ba ni da su a hannuna ba, ina tsayawa a kan iyakar kujerun da Hukumar NAHCON ta ba ni.”
Sabon shugaban hukumar ya ce sayar da kujeru fiye da wadanda NAHCON ta bayar ne “Ya sa a bara aka bar alhazan a kasa ba tare da sun tafi Kasa Mai Tsarki ba.
“Amma ni tsawon shekaru takwas da na rike Hukumar 1999-2003 da 2011-2015 ban taba barin alhaji ko daya ba. Idan ka ga mutum bai tafi ba, to sai dai idan matsalar daga gare shi ta taso,” in ji shi.
Sai dai duk kokarin Aminiya ta jin ta bakin tsohon shugaban hukumar a kan wannan magana, ya ci tura, inda ya ja bakinsa ya tsuke.