Nabila Matawalle sabuwar jaruma ce a Masana’antar Finafinan Hausa ta Kannywood da ke Kano, wadda take tashe a yanzu duk da kasancewa sabuwa a harkar.
A tattaunawarta da Aminiya, jarumar ta bayyana tarihinta da yadda ta fara harkokin fim da burinta a nan gaba.
Ki fara da gabatar da kanki.
Sunana Nabila Matawalle, an haife ni a garin Kaduna.
A can na taso, a can na yi karatun addini da na zamani daidai gwargwado.
Daga baya na koma Jihar Legas da zama, sannan daga Legas na koma Zariya domin karatu, kafin yanzu kuma Allah Ya kawo Jihar Kano aiki, inda na shiga harkokin fim a Masana’antar Kannywood.
Ina da kimanin shekara 24 yanzu.
Yaushe kika shiga harkokin fim din Hausa?
To gaskiya ban dade ba a masana’antar, sai dai zan iya cewa na shigo da kafar dama domin kwata-kwata ban wuce shekara daya ba, amma cikin ikon Allah na dan zagaye, har na kai inda ban yi tsammani ba a cikin wannan kankanin lokaci.
Sai dai godiya ga Allah kawai.
Me ya ja hankalinki kika shiga masana’antar ta fim?
Gaskiya ina da sha’awa ne kuma ina ganin ina da gudummuwar da zan iya bayarwa ta fadakarwa ga al’umma da kuma ma ilmantarwa da nishadantarwa.
Na dade ina ganin yadda jaruman suke amfani da fina-finansu wajen fadakarwa da nishadantwar, wanda haka ya sa na fara sha’awar shiga a dama da ni, amma Allah bai yi ba sai yanzu.
A ina Nabila ta fara yin fim?
A garin Kano na fara sai dai fina-finan sun kai ni gaba da Kano.
Kuma Allah kadai Ya san ina harkar za ta kaini a gaba.
A wane kamfani ne kike aiki ko kuma kika shiga yanzu?
Ina aiki ne da Kamfanin Kanawa Film Productions, kuma daraktana shi ne Adam M. Adam Trooper.
Wane fim ne kika fara da farko kuma yaya kika ji da aka fara dora miki kyamara?
Wani fim ne mai suna Kasata ne fim din na fara fitowa, inda na fito a matsayin jami’ar tsaro.
A fim din ne aka fara daura min kyamara, kuma gaskiya na yi mamakin yadda na dauka.
Ka san sha’awar abu na sa abin ya zo da sauki.
Sannan kuma kasancewar daraktan da sauran jagororin fim din suna taimakawa wajen saukake nauyin aikin wajen karfafa gwiwa, sai aikin ya yi min sauki sosai.
Zuwa yanzu kin yi fina-finai za su kai guda nawa?
Na yi fina-finai guda 9 zuwa yanzu, kuma akwai wasu da suke tafe.
A cikinsu wanne ne za ki iya cirewa a matsayin wanda kika fi so?
To a gaskiya na fi son fim din da na fito a jami’ar tsaro, wato fim dina na farko wato ‘Kasata’ saboda na wahala kwarai kuma na taka muhimmiyar rawa a fim din.
Sannan tsarin fim din yana matukar burge ni.
Sannan ina son fim din ‘Babbar Tawaga’ sosai saboda ya fi shahara.
Sannan yawancin jama’a ma cikin fim din ne suka san ni kuma a cikinsa ne na fara haskawa a idon duniya.
Akwai wani fim da kika yi jama’a suka kalla ya zama abin ce-ce-ku-ce a gare ki?
Babu Fim din da nayi ya zama kalubale gare ni ko da zan ce na samu kalubale gare shi. Gaskiya babu. Kuma in sha Allah ba za a samu ba.
Lokacin da kika bayyana wa manyanki aniyarki ta yin fim, ko kin samu matsala da su lura da cewa wasu ba so ’ya’yansu musamman ma mata suna shiga fim?
Gaskiya a kowace ma’amala da mutum zai yi da jama’a akwai kalubale amma ni ban samu ba daga wajen iyayena ko mashawartana.
Gaskiya kalubale ba za a rasa ba, amma Alhamdulillahi na samu fahimta ta iyayena tare da addu’arsu gareni.
Sun fahimce ni sannan kuma suna ganin abin da nake yi na fadakarwa ne na kuma suna musu abin da duk mutum yake yi yadda ya dauki sana’a haka take tafiya da shi.
A bangaren nasarori fa?
Gaskiya Alhamdulillah nasarori ina kan samu domin duk abin da na nema ina samu ba ni da wata matsala sannan kuma duk lokacin da aiki ya taso za a kira ni zan je in yi kuma ban taba samun matsala da kowa ba.
Duk da cewa ba ki dade ba a masana’antar, ko kina da wasu shawarwari da kike ganin za su taimaka wajen inganta masana’antar?
Gaskiya abin da ni dai na fahimta a matsayin ba da shawara a matsayina na jaruma a cikin masana’antar ita ce kawai watakila ita ce a rika lura wajen daukar jaruma ko jarumai da shekarunsu bai kai ba.
Sannan a rika tabbatarwa ana samun amincewar iyayensu na gaskiya ko kuma wani makusanci na gaskiya da zai tsaya mata.
Sannan a gindaya mata sharuda da dole ta bi su, sannan dole ta rika girmama na gaba da ita.
Kina da buri nan gaba ke ma ki zama kina sharya fim na kamfaninki?
Sosai ma kuwa ina da wannan burin kuma in Allah Ya yarda zan cika burina.
Batun iyali fa?
Wannan yana kan layi sai idan lokaci ya yi.
Wane ne gwaninki a Kannywood?
Adam M. Adam Trooper shi ne gwanina shi ne kuma daraktana.