✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kannywood: Ummi Zee-zee tana ‘yunkurin kashe kanta’

Jarumar ta ce tana cikin wani hali da tsananinsa ya sa ta fara tunanin kashe kanta

Tsohuwar jaruma a masana’antar Kannywood Ummi Ibrahim, wadda aka fi sani da Ummi Zee-zee ta bayyana cewa tana cikin kunci da ke iya zama ajalinta.

Ummi Zee-zee ta wallafa hakan ne a shafinta na Instagram, inda ta ce kuncin rayuwar da take ciki ya sa ta fara tunanin kawo karshen rayuwarta.

“A wadannan kwanaki ina cikin kuncin rayuwa, tsanani abin ya sa har na fara natunanin in kashe kaina da kaina.

“Amma ina rokon kada kowa ya tambaye ni dalili, abin da nake bukata a gare ku, ita ce addu’a,” inji sakon da ta wallafa.

Ko mene ne ya yi zafi har jarumar ta wallafa irin wannan sako?

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin jarumar ta waya, amma ba ta daga waya, sai dai ta turo wa Aminiya rubutaccen sako cewa, “Ka taya ni da addu’a”.

Tun bayan da Ummi Zee-zee ta wallafa sakon, makusanta da masoya ke ta yi mata jaje da addu’o’i gami da nasiha kan yanayin da ta tsinci kanta a ciki.

%d bloggers like this: