✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kannywood: Jarumi Malam Lawan na nan a raye

Tijjani Gandu ya tabbatar da cewa jarumin barkwanci Malam Lawan yana nan a raye

A ranar Lahadi ne labarin rasuwar jarumin barkwancin fina-finan Hausa, Malam Lawan ya karade kafafen sada zumunta.

Sai dai labarin rasuwar tasa ya zamo labarin kanzon kurege.

Tun farko mawaki Tijjani Gandu ne ya fitar da sanarwar rasuwar jarumin a shafinsa na Instagram, wanda hakan ya sa wasu daga cikin jaruman Kannywood suka shiga yin ta’aziyya da alhini.

Tijjani Gandu, cikin wani bidiyo da ya fitar a ranar Litinin ya bayyana yadda lamarin ya kasance.

“Sanarwa ta gabata a jiya cewar Malam Lawan ya rasu, to lamarin ba haka yake ba, jiya ne aka kira ni daga ofis aka ce an zo sanar da ni rasuwarsa.

“Wanda ya zo da wannan sako amininsa ne, na kira shi kuma ya tabbatar min da cewa sakon tes aka tura masa da wayar Malam Lawan din kuma kaninsa ya tabbatar masa.

“Kun ga wannan magana ce sahihiya, kuma ni ma na kira wayar Malam Lawan ya fi sau 50 tana shiga ba a dauka ba.

“Wannan idan ma kuskure ne daga wajensu ba mu san dalilinsu na yin hakan ba.

“Wannan abu ba gaskiya ba ne kuskure aka samu, ina ba wa mutane hakuri, Allah Ya datar da mu,” a cewar Gandu.

Wakilinmu ya kira jarumin ta wayar tarho don jin ta bakinsa kan lamarin, amma bai daga waya ba ballanta ko amsa sakon da aka tura masa.