✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kannywood ba wurin neman suna ba ne – Samira Saje

Rukayya Suleiman Saje wadda aka fi sani da ‘Samira Saje’, tana daya daga cikin jarumai masu tasowa, ba ta dade da shiga harkar fim ba,…

Rukayya Suleiman Saje wadda aka fi sani da ‘Samira Saje’, tana daya daga cikin jarumai masu tasowa, ba ta dade da shiga harkar fim ba, amma ta yi manyan fina-finan, inda a yanzu ta shiga sahun jarumai mata masu yawan masoya. A hirar da ta yi da Aminiya ta bayyana yadda ta shiga harkar, ranakun farin ciki da kuma na bakin ciki a harkar. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Tarihin rayuwata
An haife ni a garin Jalingo da ke Jihar Taraba a shekarar 1994. Bayan na kammala makarantar firamare da sakandare a Jihar Taraba ne na fara harkar fim, saboda burin da nake da shi na in yi karatun boko sai na sake koma wa makaranta. A yanzu haka ina karanta kwas din Aikin Banki da Al’amuran kudi a Kaduna Polytechnic. Ba a Kaduna nake da zama ba. Burina tun ina karama shi ne in yi karatu, sannan in dogara da kaina, shi ya sa bayan na fara harkar fim na sake koma wa karatu.
Yadda na fara harkar fim
A lokacin da nake karama kullum burina in samu damar da zan bayar da gudunmuwata, dalilin haka na samu karsashin kallon fina-finan Hausa, sannan na rika tunanin samun kaina a cikin masana’antar. A lokacin da nake firamare ne na sanar da iyayena niyyata ta shiga harkar fim, suka ce mini ba laifi ba ne, amma in tabbata na mayar da hankalina wajen karatu. Suka ce za su bar ni in zama jaruma matukar na kammala sakandare. Bayan na kammala sai na same su a kan alkawarin da suka yi mini, suka amince suka hada ni Tijjani Faraga, wanda da ma dan uwanmu ne. Ta dalilinsa ne na zama jaruma, inda na fara da fim din ‘Farin Wata’. Bayan na fara zama ’yar gari a harkar ne na fahimci masana’anta ce da ke samar da kudi, kuma wata kafa ta ilimantar da mutane da nishadantar da su da kuma fadakar da su. Da farko ina yi wa masana’antar kallon wurin da mutum zai nemi suna, ya kuma yi nishadi ne. A takaice na shiga harkar fim ne da amincewar iyayena, kuma su ne suke ba ni shawarwarin da suke kara mini kaimi a masana’antar.
Rana ta farko a masana’antar
Kafin in shiga harkar fim, na samu labarai iri-iri dangane da harkar, wadansu masu dadi, wadansu kuma marasa dadi. Hakan bai karya mini gwiwa ba, domin na yarda da cewa a kowace harka ta rayuwa akwai nagari da kuma bata-gari. Ya rage na mutum ya zabi abin da ya fi masa. Bayan na shiga harkar ne sai na ce dole in zama jakadar gidanmu da jiharmu ta kwarai a harkar, daga baya na fahimci irin munanan labaran da ake yadawa dangane da masana’antar ba haka suke ba, ana farfaganda. Na hadu da mutanen kirki da suke gudanar da sana’a mai tsabta. Na kuma hadu da mutanen da suke neman halaliyarsu. Na fahimci masana’anatar ba ta mayar da kai mutumin banza, sai idan ka zabi hakan. Ba ta kuma sanya ka yi abu da karfi.
Fitowa a fim
Kamar yadda na fada a baya, fim dina na farko shi ne ‘Farin Wata’, sai ‘Azima’ da ‘Maja’ da ‘Har Da Mijina’ da ‘Laifina’ da ‘Dandalinmu’ da sauransu.
Ranakun farin ciki a harkar
A wurina kowace rana a masana’antar fina-finan Hausa ta farin ciki ce, ina farin ciki da soyayyar da masoyana suke nuna mini. Nakan ji farin ciki marar misaltuwa idan na taka muhimmiyar rawa a rol din da aka ba ni.
Ranakun da ba zan mantawa da su ba
A matsayina ta jaruma ba zan taba manta ranar da muke wurin daukar fim bam ya tashi ba, bam din ya tashi a kusa da wurin da muke daukar fim ne. Abin ya faru ne lokacin da muke daukar fim a Kano. Na kadu sosai, hakan ya sanya aka kwantar da ni a asibiti na wadansu kwanaki. A wurina abin tashin hankali ne, domin ban taba jin kara mai razanarwa kamar ta wannan karon ba.
Shawara ga ’yan fim
Babban abin da yake damunmu a masana’anatar fina-finan Hausa shi ne, ba mu san rawar da ta kamata mu rika takawa a cikin al’umma ba. Su fahimci duk wanda ya yi suna to akwai ayyukan da suka rataya a kansa, domin jama’a suna kallon abin da yake aikatawa ne, domin ka zama musu mutum abin koyi, za su rika kwaikwayar kalamanka da kuma ayyukanka. Abin bakin cikin shi ne kadan daga cikin jarumai ne suka fahimci hakan, har suke taka tsan-tsan wajen kare sunan da suka yi, wanda hakan ne ya sanya wadansu suke jawo wa masana’antar abin kunya. Ina fata za mu fahimci nauyin da yake kanmu, sannan mu rika amfani da sunan da muka yi ta kyakkyawar hanya.