Akeem Yekini, shi ne kanin marigayi shahararren dan kwallon Najeriya Rashidi Yekini wanda ya rasu kimanin shekara hudu da suka gabata. kanin nasa Akeem, dan kimanin shekara 30, a tattaunawar da ya yi da kafar sadarwar intanet ta Naij.com wacce Aminiya ta ci karo da ita a yanar gizo kuma ta fassara za a ji yadda matashin tare da mahaifiyarsu suke rayuwar kunci a halin yanzu. Hasalima matashin ya ce a yanzu babu abin da yake yi wanda ya wuce tura baro don rufawa kansa da na mahaifiyarsu asiri. Ya ce sun fada wannan tasku ne sakamakon rasuwar wansa marigayi Rashidi Yakini. Ga yadda hirar ta kasanc
Tambaya: Mun samu labarin kai ne kanin marigayi Rashidi Yekini, ko za ka gaya mana yadda rayuwa ta kasance a gareka bayan mutuwar yayanka Rashidi Yekini kimanin shekara 4 da suka gabata?
Akeem: A gaskiya, marigayi Reshidi Yekibi shi ne jigon kula da gidanmu baki daya a lokacin da yake raye. Hasalima shi yake samar mana da abubuwan jin dadin rayuwa kama daga abinci zuwa tufafi zuwa duk wadansu bukatunmu na yau da kullum amma yanzu abubuwa sun yi mana zafi.
Tambaya: Ko za ka kara yi mana bayani a kan abin da kake nufi da abubuwa sun yi muku zafi?
Akeem: Abubuwan rayuwa sun yi mana zafi mana. Ina nufin yanzu da kyar muke samun na abinci a kullum ballantana a yi maganar tufafi da sauran abubuwan jin dadin rayuwa don lokacin da yake raye abubuwa ba haka suke ba.
Tambaya: To aikin me kake yi a lokacin da Rashidi Yekini yake raye?
Akeem: A wancan lokaci ina harkar kasuwanci ne watau ina saye da sayarwa.Nakan ziyarci garuruwa da kasuwanni don saye da sayarwa. Ana cikin haka ne sai kwatsam wata rana barayi suka tare mu kuma suka yi mana fashi da makami. Nan fa suka yi mini karkaf, duk jarin da nake da shi ya salwanta. Tun daga wannan lokaci ne na shiga halin tasku. Kodayake a wancan lokaci wana Yekini yana raye inda ya yi alkawarin zai sake ba ni wani jarin don na cigaba da harkar kasuwancina amma sai Allah Ya dauki ransa kafin ya cika mini alkawarin. To tun daga wannan lokaci ne na fara shiga matsala.
Tambaya: Tun bayan rasuwarsa, ko akwai wanda ya yi alkawarin taimaka wa iyalinku daga cikin abokansa?
Akeem: Eh, da yawa daga cikin abokansa sun yi alkawawarin taimaka mana, amma har yanzu da muke wannan hira da kai shiru kake ji kamar an shuka dusa.
Tambaya: Kawo yanzu wa ke kula da mahaifiyarku, ina nufin wanda yake daukar dawainiyarta musamman ga shi ta tsufa?
Akeem: Ni ke kula da ita da dan abin da nake samu daga yin kwadago. Sannan kanwata ma tana taimaka wa wajen kula da ita sai dai ita ma kanwar tawa ta rasu ne a wani hadarin mota a hanyarta ta zuwa wajen kanin mahaifinmu don karbo kudin da za a kula da mahaifiyar tamu. Hadarin ne ya yi sanadiyyar rasuwarta.
Tambaya: Kana nufin ita ma kanwarka ta rasu ne a kokarin ganin ta tallafa wa mahaifiyarku?
Akeem: kwarai da gaske. Abin bakin cikin ma shi ne yadda ta rasu ita ma ta bar ’ya daya da dawainiyarta ya sake hawa kaina. Don haka ne na zage damtse nake yin kwadago don neman abin da za mu rufa wa kai asiri.
Tambaya: Kawo yanzu Hukumar shirya kwallon kafa (NFF) ta tuntube ka ko mahaifiyarku don sanin halin da kuke ciki?
Akeem: Gaskiyar magana ita ce har yanzu babu wani jami’i daga Hukumar NFF ko daga bangaren gwamnati da ya tuntube mu ko ya tuna da mu. Mu dai kawai mun dogara ne daga abin da Allah Ya hore mana wajen kula da kanmu.
Tambaya: Yi mana bayani a kan abubuwan da kake yi a halin yanzu wajen samun kudin shiga.
Akeem: Babu abin da nake yi da ya wuce tura baro, don ina ganin shi ne hanya mafi sauki da zan samu aikin yi ba tare da na je ina yi wa mutane ’yar murya ba. Na nemi aikin gwamnati ko na kamfani a baya, amma abin ya ci tura.
Tambaya: Ka ce ka nemi aikin gwamnati, ka yi karatu ne?
Akeem: Na taba karatu, don yanzu ina da shaidar karatu na matakin satifiket ne, duk da ba karatu mai zurfi na yi ba.
Tambaya: Yanzu idan ka samu dama za ka iya yin kwallo a wani kulob?
Akeem: kwarai da gaske da zan samu dama, zan iya buga kwallo a kowane kulob. Amma babbar matsalar ita ce ko ina da kudin da zan sai kayayyakin kwallo irin su takalmi da riguna da wanduna da safuna da sauransu, ai ba zan kwashi kudin in je in sayo irin wadannan kayayyaki ba, alhali muna fama da yunwa da talauci a gida. Na gwammace na sayo kayan abinci da za mu dade muna amfani da shi a gida akan na yi amfani da kudin wajen sayo kayayyakin wasanni.
Tambaya: Yanzu wane taimako kake so a yi maka, kuma idan wani ko wasu sun nemi su taimaka maka, kana da lambar asusun ajiya ne (Bank Account Number)?
Akeem: Ina rokon ’yan Najeriya su dubi Allah su ceto mu daga cikin kuncin rayuwar da muka tsinci kanmu a ciki. Kuma gaskiyar magana ita ce ba ni da lambar asusun ajiya irin ta banki watau (Bank Account). Asusun ajiyar da nake da shi bai wuce na wani bankin da ke yankinmu ba watau Community Bank, ka ga kuma ba ko’ina za a iya aiko maka da kudi ko wani taimako kai tsaye ta ciki ba. Sannan maganar asusun ajiya ba sai mutum ya koshi, ya ci ya rage sannan zai fara tunanin ajiye rara ba? To ni halin da nake ciki ba zai taba ba ni damar yin ajiya ba, don hannu-baka-hannu-kwarya nake yi.