✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kanawa har yanzu suna jiran Buhari

A ranakun Laraba da Alhamis 6 zuwa 7 ga wannan watan da muke ciki Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu gagarumar maraba a cikin ziyarar…

A ranakun Laraba da Alhamis 6 zuwa 7 ga wannan watan da muke ciki Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu gagarumar maraba a cikin ziyarar yini biyu da ya kai Jihar Kano. Ziyarar da aka dade ana jira, har ta kai ‘yan adawa na cewa shugaban kasar ba zai ziyarci jihar ba, musamman ganin an sa ranar 27 ga watan Nuwamba da ya gabata, amma kuma aka daga. Ziyarar a bisa ga al’ada ta ba shugaban kasa damar kaddamar da wasu ayyukan raya kasa da duba wadanda ake kan aiwatarwa da Gwamnatin Gwamnan jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje ko dai ya kammala ko kuma yake da aniyar aiwatarwa. Shugaba Buhari kuma ya yi amfani da ziyarar wajen bude wasu manya-manyan masana’antu da suke sarrafa amfanin gona a jihar ta Kano.

Daga cikin ayyukan da Shugaba Buhari ya kaddamar sun hada da manyan asibitocin nan biyu da Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau ta fara, wato asibitin kwararru na unguwar Giginyu da aka sanya wa sunan asibitin kwararru na Muhammadu Buhari da kuma asibitin kananan yara na kan titin zuwa gidan zoo. Gwamna Ganduje ya fadi cewa gwamnatinsa ta kashe makudan biliyoyin Naira wajen kayata asibitocin da na’urori irin na zamani da ba irin su a dukkan fadin kasar nan, haka ma sauran ayyukan raya kasar da ta gudanar irinsu gina gadar kasa ta dorayi da ci gaba da aikin ginin gadar sama da ta taso daga Koka-Kola zuwa masallacin Juma’a na Fagge ta fara gina gadar kasa ta kusa da Barikin sojoji.

 Shi ma Shugaba Buhari a cikin jawabinsa a lokuta daban-daban da yake kaddamar da bikin bude asibitocin ya yaba wa Gwamna Ganduje bisa ga wadannan muhimman ayyuka da ya gabatar, kuma wadanda yake kan gabatarwa don amfanin al’umma, yana mai nuni da cewa hakan shi ne akidar CANJI na jam’iyyarsu ta APC, kuma sai ya yi fatan sauran gwamnoni za su yi koyi da ayyukan alheri na Gwamna Ganduje. 

Shugaba Buhari a ranar farko ta ziyarar da ya kaddamar da wadancan ayyuka ya kuma kai ziyara babban gidan kurkuku na Kurmawa da ke cikin birnin Kano, inda ya yi afuwa ga wasu fursunoni 500, da bayan afuwar da ya yi musu, ya kuma ba su wasu ‘yan kudi a zaman tallafi. Akasarinsu wadanda aka yi wa afuwa matasa ne masu kananan shekaru, ya kuma yi amfani da damar ziyarar gidan kurkukun na Kurmawa wajen duba aikin ginin da ake fadada gidan kurkuku. 

A yayin ziyarar ban girma ga Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammdu Sanusi na II, Shugaba Buhari ya bayyana matukar gamsuwa da jin dadi a kan irin gagarumar maraba da Kanawa suka yi masa, yana mai cewa hakan ya nuna masa zai iya kara cin zabe nan gaba a jihar ta Kano, abin da ya ce ya nuna cewa mutanen jihar suna sane da irin muhimman ayyukan da gwamnatinsa ta sa a gaba, irin na inganta matakan tsaro da farfado da tattalin arzikin kasa da yaki da cin hanci da rashawa, abubuwa ukun da ya ce su dama jam’iyyarsu ta APC ta yi wa ‘yan kasa alkawarin aiwatarwa a lokacin yakin neman zaben shekarar 2015. Ya kuma yi waiwaye akan alakarsa da masarautar Kano, wadda ya ce tsohuwar alaka ce, ta yadda duk abin da ya yi a rayuwa akwai gudummuwar masarautar. 

Yayin da ya ke mayar da martani a zaman maraba lale ga Shugaba Buhari, Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi na II, bayan ya yi wa Shugaba Buhari kyakykyawan fatan alheri a bisa ga mulkinsa, sai kuma ya yi fatan badi warhaka in Allah Ya kaimu Shugaba Buhari zai dawo Kano don ya kaddamar da ayyukan raya kasar da gwamnatinsa ka bijiro wa mutanen jihar don ci gabansu. Jawabin na mai martaba akan neman wannan bukata ya samu fassarar masu fashin baki da nazarin al’amurran yau da kullum, tamfar hannunka mai sanda sarkin ya yi wa Shugaba Buhari ko matashiya a kan duk fa da irin yadda mutanen jihar suka yi wa Shugaba Buhari ruwan kuri’u a kakar zabe ta 2015, har yanzu muatnen jihar ba su gani a kasa ba ayyukan jin dadin rayuwa da Gwamnatin Buharin ta aiwatar musu. 

A dai yayin waccan ziyara Shugaba Buhari ya yi amfani da damar wajen bude wasu maka-makan masana’antun sarrafa amfanin gona a Kano, wadanda aka ce ba kamarsu a nahiyar mu ta Afirka ta Yamma kaf. Masana’antu su ne na masana’antar yin man girki ta Gerawa da ke Tokarawa kusa da Kano, masana’antar da ke iya sarrafa tan 1,200, na waken soya duk rana, da kuma yin abincin kaji. Shugaba Buhari ya fadi cewa canjin da ake samu yanzu a kan harkokin kasuwanci da zuba jari a gwamnatinsa zai taimaka wa kasar nan aniyar da ta ke da ita wajen kara zakulo hanyoyin samun kudaden shiga a ciki da wajen kasar nan, ba tare da ci gaba da dogaro da man fetur ba.

Shi ma da yake nasa jawabin shugaban masana’antar man girkin ta Gerawa Alhaji Isa ya yaba wa Gwamnatin Buhari a bisa ga tsare-tsarenta na ganin ingantuwar ayyukan noma, yana mai kira ga gwamnatin da ta hanzarta duba, tare da inganta hanyoyin samar da bashin ayyukan noma da kuma masu masana’antun da suke sarrafa amfanin gona a kasar nan. Wata masana’antar sarrafa amfanin gona da Shugaba Buhari ya kaddamar ita ce ta sarrafa shinkafa ta Fullmark da ke kwanar Gunduwawa a kan titin Hadeja.

Kodayake a duk tsawon ziyarar Shugaba Buhari ta yini biyu, duk da irin tarurrukan da ya rinka yi da masu ruwa da tsaki na jihar wato ‘yan kasuwa da Ulama’u da ‘yan siyasa da ‘yan kwadago da na kungiyoyin kare hakkin dan Adam, ba inda aka ji shugaban ya bayyana takamaimai matsayin abin da gwamnatinsa za ta yi a kan irin bukatun da jama’ar Jihar Kanon da sarkinsu suka nema. 

Alal misali bayan wancan fata da mai martaba sarki ya yi na Allah Ya kaimu badi shugaban kasa ya dawo ya kaddamar da ayyukan raya kasa da gwamnatinsa za ta yi wa mutanen jihar. An ce ma a taron da ya yi da Ulama’u an nemi jin yiwuwar gwamnatinsa ta rage tsadar da kudaden zuwa aikin hajji suka yi, amma an ce sai shugaban a takaice ya ce da su aikin hajji na mai hali ne kamar yadda shari’ah ta shinfida. ‘Yan kasuwanni biyar na cikin birnin Kano da kewaye da suka yi fama da iftila’in gobara a lokuta daban-daban daga watan Fabrarun 2016, wadanda da kuma gwamnatin jihar ta fara raba wa tallafin kashi 5 cikin 100, na abin da suka yi asara a jajibirin ziyarar shugaban kasa sun yi tsammanin jin irin gudummuwar gwamnatin tarayya daga bakin shugaban kasa, amma sai suka ji shugaban ya yi gum da bakinsa.

Duk da rashin jin wani abu takamaimai akan bukatun mutanen Jihar Kanon daga bakin shugaban kasa a yayin ziyarar, ka iya cewa ziyarar ta samu gagarumar nasarar da ba a tsammani, kasancewar kafin ziyarar musamman daga kalaman ‘yan adawa da su ke cewa shugaba Buhari ba zai sakawa mutanen jihar ba, bisa ga karamcin da suka yi masa na fitowarsu kwansu da kwarkwatarsu suka zabe shi a kakar zaben shekarar 2015. Da wannan ka iya cewa Kanawa, har yanzu suna jiran Buhari.