‘Yan kasuwa masu sayar da ‘Yan kunne da sarka karkashin kungiyarsu ta Jedda (Jewelries Dealers Debelopment Association da ke Jihar Kano sun koka game da rashin samun wani tallafi daga gwamnatin jihar, inda suka nemi gwamnati da ta tuna da ‘ya’yan wannan kungiya musamamn marasa karfi ta kawo musu dauki don dorewar kasuwancinsu.
Alhaji Jahi Abdullahi shi ne Sakataren wannan kungiya ya bayyana wa Aminiya cewa duk da irin ikrarin da gwamnati ke yi cewa tana tallafa wa kananan ‘yan kasuwa, har zuwa yanzu ‘ya’yan kugiyarsu bas taba amfana da irin wannan tallafi ba, duk kuwa da kiraye-kirayen da suke ta yi ga gwamnatin akan hakan. “Muna bukatar gwamnati ta tallafa wa masu karamin karfi da jari, kamar yadda take yi ga sauran bangarori a jihar. Mun sha yin kira ga gwamnati akan akan, to ba mu sani ba ko kiran namu ne bai zuwa kunnenta. Don haka muke amfani da wannan kafa don yin kira ga gwamnati”
Da yake bayyana ayyukan da kungiyarsu ke yi wajen taimakon kai da kai Sakataren ya ce “mu akan kanmu daga dan abin da muke samu yayin yi wa ‘ya’yan kungiyarmu rajista da kuma dan abin da muke hadawa a tsakaninmu shugabanni mukan taimaka wa yan kasuwarmu a duk yayin da wasu matsaloli suka taso. Misali na rashin lafiya, mukan biya kudin magani , domin a kwanan nan mun biya wa mamba dinmu Niara dubu 100 aka yi masa aiki. Ban da taimakon Naira dubu 30 zuwa 20 wannan ba a lissafawa. Haka kuma idan wani daga cikin ‘yan uwanmu ya rasu mukan sayi kayan abinci mu kai wa iyalinsa don rage radadin halin da suke ciki”.
A cewar Sakataren baya ga taimako na kudi sukan tsaya wa yayansu a dk lokacin da suka shiga wani rikici na ciniki. “idan har wata rigima ta kasuwnci ta tasowa wa yayanmu muna shige masa gaba har sai an warware ian ta kai ga kotu ma muna da lauyan da muke turawa ya tsaya masa idan mun tabbatar yana da gaskiya. Sannan kasancewar kasuwacinmu ya shafi tafiya musamamn zuwa Legas idan wani abu ya taso ya hada da dan uanmu mukan tashi wakilanmu don zuwa a sasanta lamarin. Haka ma a cikin kasuwa idan wata rigima ta taso mukan sulhunta tsakanin ‘yan kasuwa da ‘yan kasuwa ko kuma tsakaninsu da kwatomominsu. Haka kuma Sakataren ya yi kira ga gwamnati da ta kawo karshen matsananciyar wahalar rashin wutar lantarki da ake fama da ita a gaba dayan Kasuwar Sabon Gari. “Tun bayana da aka yi gobara ba mu sake samun wutar lantarki a kasuwa ba, sai dia janareto ko sola da ’yan kasuwa ke yin amfani da su a kullum. An sha zaunawa tsakanin hukumar kasuwa da ‘yan kasuwa akan wannan batun, inda ’yan kasuwa suka nuna sun fi son wutar da ake kira maja wacce wasu jama’a ke samar da ita, saboda ‘yan kasuwa suna zargin ana samun tashin gobara ne ta hanyar wutar lantarkin da aka saba da ita. A lokacin gwamnati ta amince da rokon yan kasuwa inda wasu kamanoni masu zaman kansu 11 suka nemi za su samar da wutar, sai dai har zuwa yanzu duk da gwamnatin ta amince, amma ba ta ba su izinin fara aikin ba. don haka muke roko gareta da ta duba wannan lamari domin ’yan kasuwa suna cikin wani hali.’