✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kananan ‘yan kasuwa sun fara samun tallafin GEEP

Kimanin kananan ‘yan kasuwa 200 ne suka amfana da tallafin jarin kudin  nan na tallafi ga kananan ‘yan kasuwa (GEEP a daidai lokacin da Karamin…

Kimanin kananan ‘yan kasuwa 200 ne suka amfana da tallafin jarin kudin  nan na tallafi ga kananan ‘yan kasuwa (GEEP a daidai lokacin da Karamin Bankin Kasuwanci na Grassroot Micro finance bank da ke Jihar Kano ya kaddamar da fara raba kudin a karo na farko. Shi dai wannan tallafi  na GEEP Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ce ta bullo da shi da niyyar bayar da jari ga kananan ‘yan kasuwa  wadanda suka hada da mata ‘yan kasuwa da matasa masu sana’a da kuma manoma.

Hajiya  Farida Ahmed Tahir ita ce Manajan Bankin Grassroot ta shaida wa Aminiya cewa gwamantin tarayya ta ba Bankin Masana’antu alhakin raba kudin inda shi kuma bankin ya hada kai da kananan bankuna da ke fadin kasar nan don ganin wadanda aka yi dominsu sun kai ga samin kudin.

A cewarta Bankinsu ya cika duk sharudda da kaidojin da Bankin Masana’antu ya gindaya inda a kashi na farko aka ba su Naira miliyan 25 don raba wa ga jama’a. “Kamar yadda manufar shirin take don tallafawa kananan ‘yan kasuwa, wanda kuma sanin kowa ne bankuna irin namu ne ke mu’amala kai tsaye da kananan ‘yan kasuwa hakan ya sanya Bankin Masana’antu ya gayyato mu inda ya sanya sharrudansa. Bayan mun cika sharruddan ne sai Bankin ya ba mu Naira Miliyan 25 don raba wa ga wadanda suka cancanta”

A cewarta mafi yawan kudin da mutum zai iya karba a matsayin bashin shi ne Naira dubu 100 haka kuma karancin kudin da mutum zai iya karba na tallafin shi ne Naira dubu 10

Manajan ta yi kira ga jama’a wadanda ke da sha’awar karbar kudin da su yi hanzarin yin hakan ta hanyar hadin kai da kungiyoyi, kasancewar ba a ba wa daidaikun mutane kudin. Har ila yau Manajan ta yi kira ga sauran takwarorin bankuna irin nau da su yi kokarin cika kaidojin da Bankin Masana’antu ya sharadtan don karbar kudin da za su raba ga jama’a “ya kamata Jama’a su fahimci cewa kudin nan suna da yawa domin a shekarar farko Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 112 wanda ake sa ran raba su ga mutum miliyan daya da rabi a dukkanin kananan hukumomi 774 da ke fadin kasar nan, don haka wannan dama ce da bai kamata sauran bankuna irin namu da sauran al’umma su yi wasa da ita ba don ganin sun ci gajiyar shirin. ”

Mafi yawan  wadanda suka amfana da tallafin sun nuna farincikinsu tare da godiya ga Shugaabn Kasa Muhamamdu Buhari tare da alkawarin mayar da kudin kamar yadda yake a cikin takardar yarjejeniyar. Hajiya Hajara Muhammad mazauniyar Karamar Hukumar Nassarawa wacce ke sana’ar sayar da kayan gwanjo ta bayyana cewa “muna godiya ga Shugaban kasa bisa wannan tallafi da aka ba mu, duk da cewa dai ba shi ne, amma mun gode kwarai domin zai taimaka mana kwarai wajen kara bunkasa sanaoinmu, wanda dama yawanci muna fama da matsalar rashin jari a hannu, mun gode. Allah ya ba Shugaban kasa lafiya. Allah Ya ba mu ikon biya kamar yadda muka karba cikin farin ciki”.