✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sana’o’i: Gwamnati ta fara rabon tallafin N30,000

Masu nasa'o'in hannu guda 333,000 ne za su samu N30,000 kowannensu

Gwamnatin Tarayya ta fara rabon tallafin N30,000 ga masu  sana’o’in hannu a jihohi domin rage musu radadin annobar COVID-19.

Masu nasa’o’in hannu 333,000 za su samu N30,000 kowannensu da nufin rage musu tasirin COVID-19 karkashein shirin tallafin gwamnati na Survival Funds.

Akalla mutum 9,00 ne a kowace jiha za su ci gajiyar shirin wanda ke bukatar su mallaki shaidar tantance asusun ajiyar banki da lambar shaidar zama da kungiyar sana’ar da suke yi.

Wadanda za su ci gajiyar kudaden sun hada a teloli, direbobi, kwandastoci, birkiloli, ‘yan baro, ‘yan acaba da dangoginsu

An fara rabon kudaden ne a Jihohin Kano, Kaduna, Borno, Bauchi, Legas, Abuja, Filato, Ekiti, Abia, Ribas, da kuma Delta.

Minista a Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Ambasada Mariam Yelwa Katagum ta ce kashi 45 cikin 100 na masu samun tallafin mata ne.

Ta byyana yaka ne a lokacin kaddamar da rabon tallafin a Abuja a ranar Alhamis a yayin bikicin cikiar Najeriya shekara 60 da samun ‘yancin kai.

A ranar 9 zuwa 31 ga watan Oktoba za a yi rabon tallafin a jihohin da ke a rukuni na biyu da suka hada da Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Edo, Ogun, Ondo, Inugu da Ebonyi.

Jihohin da ke rukuni na uku kuma za su samu nasu ne daga ranar 9 zuwa 21 ga Nuwamba, 2020 a Jihohin Zamfara, Yobe, Sokoto, Nasarawa, Jigawa, Gombe, Binuwai, Neja, Akwa-Ibom, Kuros Riba, Imo, Oyo da Osun.