Kungiyar Kamfanonin Sufurin Jiragen Sama ta Kasa ta ce za ta dakatar da ayyukansu daga ranar Litinin mai zuwa saboda tashin gwauran zabon da farashin man jirgi ya yi.
Bayanin hakan ya fito ne ta wata wasika da Shugaban kungiyar, Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina ya aika wa Ministan Sufurin Jiragen sama, Hadi Sirika.
- Daukar hoto tsirara a gaban ‘bishiya mai tsarki’ ya jawo wa ’yan Rasha kora daga Indonesia
- Dan siyasa ya yi murabus saboda kallon bidiyon batsa a zauren Majalisa
Kungiyar ta nemi afuwar fasinjojinta inda ta ce tsadar man ce ta sanya aka samu karin farashin jigila da fiye da kasi 95 cikin 100.
Man dai a yanzu lita daya ya kai Naira 700, sabanin farashinsa na baya na Naira 190.
“Dalilin haka ya sanya muke rokon Gwamnatin Tarayya, majalisar kasa kamfanin mai na kasa, masu cinikin man, da su tainaka su sakko da farashin wanda tsadarsa ta sanya jirgin da zai tafiyar awa guda ya kai kudin kujera 120,000.
“Duk da muna yabawa Gwamnatin Tarayya bisa kokarinta ne inganta bangaren sufurin jirgi, tashin farashin man ya sanya hakan ba zai yiwu ba,” inji shi.
Daga karshe sun nemi afuwar ’yan Najeriya bisa dakatar da aikin da suka yi na sai baba ta gani, har sai abubuwa sun daidaita.