✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin wayoyin lantarki na Coleman Cables ya bude daffo a Kaduna

A wani yunkuri na kawar da jabun da gurbatattun wayoyin lantarki domin samar da ingantattu ga ’yan Najeriya, kamfanin wayoyin lantarki na Coleman Cables and wires…

Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Zartarwar Kamfanin, Mista George Onafowokan, wanda ya bayyana haka a tatttaunawa ta musamman da wakilinmu a shekaranjiya Laraba, ya ce daffon na Kaduna zai kasance yunkurin fadada kamfanin a sassan kasar nan.

Mista Onafowokan ya ce: “Burinmu mu kasance a ko’ina ba kawai a wani sashi na kasar nan ba. Kuma muna duba yiwuwar bude masana’antunmu a sassa daban-daban na kasar nan. Daffon na Kaduna shiri ne na farko a yankin Arewa. Kaduna za ta sa kamfanin ya zo kusa da yankin Arewa maso Yamma.”

Ya ce, zuwa kusa da abokin ciniki yana nufin samar da kayayyakin lantarkin a farashi mai rahusa tare da tabbatar da sun samu kayayyaki na kwarai. “Wannan zai kare su daga sayen jabu ko gurbatattun wayoyin lantarki a kasuwa,” inji shi.

Shugaban ya ce, jabu da gurbatattun wayoyin lantarki suna ci gaba da samun kasuwa ne, saboda babu ingantattun wayoyin lantarki nagari a kowane lungu da sakon kasar nan, lamarin da ya sa masu fasakauri ke wahalar da jama’a. 

Mista Onafowokan ya ce: “Muna cike da farin ciki cewa kowa ya san wayoyin lantarkin da aka yi a Najeriya sun fi duk wadanda ake shigowa da su inganci. Gwamnati ta sani, suna cikin kamfe din ingancin kaya na NIS/SON da kamfanonin lantarki da SON suka kirkiro. Akwai cikakken inganci kuma wayoyin suna da cikakken inganci.

Kamfanin Coleman a wannan sana’a an san shi wajen kyakkyawan inganci da samar da kayayyaki, kuma wannan ne muke son isarwa ga jama’armu a sannan kasar nan.”