✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin NNPC ya tafka asara

Kamfanin Man fetur din kasar nan (NNPC) ya ba da sanarwar faduwar fiye da naira biliyan biyar daga abubuwan da yake samarwa, kamar yadda BBC…

Kamfanin Man fetur din kasar nan (NNPC) ya ba da sanarwar faduwar fiye da naira biliyan biyar daga abubuwan da yake samarwa, kamar yadda BBC ta bayyana.

Kamfanin wanda yake sarrafa man Diesel da kalanzir da kuma fetur, ya ce ya yi cinikin fiye da naira biliyan 38 idan aka kwatanta da fiye da naira biliyan 44 da ya samu a watan Agustan wannan shekarar.
Daga watan Janairu zuwa watan Satumbar bana, kamfanin ya samu harajin naira 46 biliyan a kan man diesel da kalanzir da kuma man fetur.
Kamfanin NNPC tun bayan da aka nada Cif Emmanuel Kachukwu ya soma bayyana irin cinikin da yake yi a harkar man fetur a wani mataki na kawar da cin hanci da rashawa a kamfanin.
Tun bayan da ya fara mulki, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kawar da barna da dukiyar al’umma a kamfanin NNPC.