✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin Huawei ya shiga jerin kamfanin waya 100 na duniya

Kamfanin kera wayar salula na Huawei ya samu nasarar shiga jerin kamfnonin sadarwa 100 da suka yi fice a duniya. Kamfanin Millward Brown Optimor da…

Kamfanin kera wayar salula na Huawei ya samu nasarar shiga jerin kamfnonin sadarwa 100 da suka yi fice a duniya.

Kamfanin Millward Brown Optimor da ya yi fice a bincike kan harkar sadarwa ya sanya kamfanin Huawei a matsayin na 70 a jerin kamfanonin.
Shugabar kamfanin Brand Z na duniya, daya daga cikin kamfanonin da suka zabi sanya ido a zaben, Mis Doreen Wang, ta ce hakan shi ne karo na farko da kamfanin Huawei ya samu nasarar shiga jerin kamfanoni 100 da suka yi fice a duniya a harkar sadarwa.
“Hakan shi ke nuna kwarewa da kuma ci gaba a harkar kasuwanci. Kamfanin Huawei ya sanya hannun jarin cikin harkar kimiyya da fasaha ta hanyar sanya jarin kashi biyu da cikin kashi uku na kudin shigar da kamfanin yake samu daga wajen kasar China a harkar sadarwa. Saboda haka sanya shi cikin jerin sunayen ya nuna irin karfin kamfanin Huawei.”
Baban manajan kasuwanci na kamfanin, Mista Olaonipekun Okumowo bayyana cewa matakin ya nuna yadda kamfanin Huawei ya karbu a duniya.
Ya ce: “Wannan abin farin ciki ne ga kamfanin Huawei. Hakan shi ke nuna cewa kamfanin wayoyin da kamfanin Huawei ke kerawa su samu karbuwa a duniya duk da irin kalubalen da kamfanonin kasar China ke fuskanta a gogayya da takwarorinsu na duniya. Saboda haka kamfanin Huawei ya himmatu wajen samar da sabuwar kirkira don dadawa abokanen huldarsa.”
Kamfanin Millward Brown Optimor da ya shirya gasar ya kasance kan gaba a binciken da nazarin kamfanonin sadarwa na duniya.
Kamfanin Huawei ya kasance kamfanin na uku mafi girma a duniya da ke kera wayar zamani a shekarar 2014.