✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin Facebook ya sauya sunansa zuwa ‘Meta’

Sauyin bai shafi kafafen sada zumunta na Facebook, Instagram da WhatsApp ba.

Mai Kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg, ya sanar da sauya sunan kamfanin zuwa ‘Meta’ a ranar Alhamis.

Sai dai ya ce sauyin bai shafi kafafen sada zumunta na Facebook, Instagram da WhatsApp ba, suna kamfanin kadai ya shafa.

Sanarwar da kamfanin ya fitar ya ce ya fadada ayyukansa ta yadda zai kunshi dukkan abubuwan da yake yi, saboda yana da abubuwan da suka zarta shafukan sada zumunta zuwa yin abubuwa na kamar a zahiri wato ‘virtual reality’.

Kazalika, kamfanin ya bayyana cewa ayyukansa za su ci gaba da kasancewa yadda suka saba.

Matakin na zuwa ne a yayin da wasu tsoffin ma’aikatan kamfanin suka fitar da wasu jerin bayanai marasa dadi ne a kan kamfanin.

Daga cikin tsoffin ma’aikatan kamfanin, Frances Haugen, ya zargi kamfanin da fifita riba a kan tsaro da maslahar mutane.