Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da sauya sunan Jami’ar Jihar Borno zuwa Jami’ar Kashim Ibrahim, domin girmama tsohon Gwamnan Arewa na farko, Kashim Ibrahim.
Wannan matsaya na zuwa ne bayan taron majalisar zartarwa na farko a shekarar 2025, wanda aka gudanar a gidan gwamnatin jihar.
- Ciyaman ya naɗa hadimai 60 a Kano
- Rikicin siyasa tsakanin Kwankwaso, Shekarau da Ganduje na hana Kano ci gaba – Garo
A yayin taron an tattauna na tsawon sa’o’i shida kan muhimman batutuwan da suka shafi ci gaban jihar.
Da yake ƙarin haske bayan taron, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Tsaro na Cikin Gida, Farfesa Usman Tar, ya bayyana cewa majalisar ta yi nazari kan takardu 42, tare da duba nasarorin 2024 da shirye-shiryen sabuwar shekarar 2025.
Ya ce sauya sunan jami’ar zai kasance ne bisa doka tare da tuntuɓar hukumomin da suka dace, ciki har da NUC, JAMB, da COREN.
A cewarsa, “Majalisar ta amince da sauya sunan Jami’ar Jihar Borno zuwa Jami’ar Kashim Ibrahim, kuma an fara aikin gyaran dokar kafa jami’ar domin tabbatar da wannan sauyi.”
Haka kuma, majalisar ta yanke shawarar sanya sunya wa tituna da gidaje a Maiduguri da sauran garuruwa suna a wani ɓangare na sabunta birane.
“A yanzu Maiduguri na fuskantar ci gaba sosai, kuma sabbin gine-gine sun buƙaci sanya sabbin sunaye domin inganta tsare-tsaren birane,” in ji shi.
Farfesa Tar, ya ƙara da cewa sabbin sunayen za a sanya su a taswirar ‘Google’ da sauran kundayen bayanai domin sauƙaƙa gudanarwa da ci gaba.
Da yake jawabi a taron, Gwamna Zulum, ya yaba wa majalisar bisa goyon bayan da suke bai wa gwamnatinsa.
Ya kuma bayyana aniyar ƙara ƙaimi wajen yaƙi da matsalolin jihar da samar da ayyukan more rayuwa a 2025.
Hakazalika, an karrama shugaban ma’aikatan gwamnati mai barin gado, Barista Malam Fannami, saboda gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jihar.