✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin bitafoam ya tallafa wa ’yan gudun hijiran Barno

Kamfanin Katifar bitafoam ya ba da tallafin katifu guda 100 da matasan-kai 100 ga mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a Jihar…

Kamfanin Katifar bitafoam ya ba da tallafin katifu guda 100 da matasan-kai 100 ga mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a Jihar Barno ta hannun kungiyar Oasis da ke aikin tallafawa jama’a a Jihar Legas.

Da yake jawabi a wurin bikin bayar da kyautukan da aka gudanar a ofishin tuntuba na Jihar Barno da ke Jihar Legas a karshen makon da ya gabata, Babban Daraktan tsare-tsare na kamfanin, Alhaji Abbagana Muhahammed Abatcha, ya bayyana cewa kamfanin ya bayar da kyaututtukan ne don ya taimaka wa mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa.
Alhaji Abatcha ya ce, “Ka san shi sha’anin kamfani kullum muna lura da abubuwan da yake faruwa a kasa baki daya kuma yanayin abubuwan da suka auku a yankin Arewa-maso-Gabas abu ne wanda yake ba gwamnati kadai za a bari da dawainiyar mutanen da rikicin ya shafa ba, dole sai an hada karfi da karfe tsakanin kamfanoni da gwamnati da mutane masu hannu da shuni su taimaka wa jama’a don mutanen da lamarin ya shafa su koma rayuwarsu kamar yadda suka saba. To shi ya sa muka ga ya dace mu hada karfi da kungiyar Oasis don mu taimaka wa jama’a.”
Ya ci gaba da cewa: “Taimakon da kamfanin ya bayar ba shi ne na farko ba, don mu sha bayar da taimako a jihohi da dama kamar wuraren da aka samu ambaliyar ruwa da annobar cututtuka da sauransu kuma kullum muna iya kokarinmu don bayar da tallafi ga al’umma don mu rage musu radadin bala’in da ya same su.”
A nashi jawabin jim kadan bayan ya mika kyauttukan ga wakiliyar jihar a Legas, Babban Manajan Daraktan kamfanin, Mista Taiwo Adeniyi ya ce kayayyakin za su rage wa ’yan gudun hijirar radadin tashin hankalin da suka shiga.
Ya bayyana cewa rikicin Boko Haram ya shafi ayyukan kamfanin bitafoam, inda kamfanin ya yi asarar kudin shiga masu yawa.
Ya yaba wa gwamnatin Jihar Barno da suka bai wa kamfanin damar taimaka wa ’yan gudun hijirar da ke sansanoni a jihar.
Shi ma a nashi jawabin, shugaban kungiyar tallafawa jama’a da ake kira Oasis Association, Iya Bayis Mashal Olufemi Soewu, ya bayyana cewa kungiyarsu ta hada kwararru a fanonin iri-iri a cikinta wadanda suke taimaka wa jama’a.
Ya ce, kungiyar ta tallafa wa mutane da yawa da bala’o’i suka afka musu a yankuna da yawa na jihohin kasar nan.
Daga bisani ya yaba wa kamafnin bitafaom saboda amsa bukatun kungiyar na tallafa wa wadanda rikicin ya raba da muhallansu a Jihar Barno cikin gaggawa.
Har ila yau, babbar jami’a a ofishin tuntuba ta jihar da ke jihar Legas, Misis Racheal Dunama Balami ta yaba wa shugabannin kamfanin katifar dangane da tallafin da suka bai wa ’yan gudun hijira a jihar. Misis Dunama Balami ta yi alkawarin isar da kayan tallafin ga Gwamnatin Jihar Barno “ba tare da bata lokaci ba.”