Wani kamfanin samar da makamashi mai suna Bagaja Renewables, ya ce ya fara aikin gwajin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana mai karfin megawat ɗaya a Kano.
Kamfanin ya ce zai samar da lantarkin ce a rukunin gidaje na Gida Dubu da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso da ke jihar.
Daraktan shirin samar da wutar a kamfanin, Sadiq Zakari ne ya sanar da hakan lokacin da wata tawagar ƙwararru ta kamfanin suka gudanar da gwajin ƙarshe na injinan da za su bayar da wutar a rukunin gidajen.
Sadiq ya ce aikin ya kuma ƙunshi duba ƙarfin injinan wutar da nauyin da za su iya ɗauka domin tabbatar da cewa an yi amfani da su yadda ya kamata wajen samar da lantarkin ga mazauna unguwar.
- Masu gasar shan kwaya a bikin aure sun shiga hannun NDLEA a Katsina
- Sanatoci sun sallama albashinsu na Disamba ga mutanen Tudun Biri
Ya ƙara da cewa, “binciken farko-farko da aka gudanar ya nuna cewa akwai alamun nasara wajen samar da wutar mai ƙarfin megawat ɗaya ga mazauna rukunin gidaje na Gida Dubu ba tare da ƙaƙƙautawa ba.”
Daraktan ya kuma ce kamfanin ya yi tsayuwar daka wajen tabbatar da magance duk wata matsala da za ta iya tasowa yayin da yake ci gaba da aikin, inda ya ba mazauna rukunin gidajen tabbacin kammala aikin a kan lokaci.
Kamfanin na Bagaja ya ce aikin wani ɓangare ne na yunƙurinsa na samar da makamashi mara gurɓata muhalli a Najeriya ba wai ga iya yankin kawai ba, har ma da wasu wuraren a nan gaba.
Kamfanin dai shi ne irinsa na farko a Najeriya da ya samar da wutar lantarki daga hasken rana da ta kai ƙarfin megawat ɗaya, kuma yana fatan ganin hakan ya bunkasa kasuwanci da tattalin arzikin yankin.
A shekara ta 2022 ce kamfanin na Bagaja ya rattaba hannu a kan yarjejeniyar da Kamfanin Rarraba Hasken Wutar Lantarki na Shiyyar Kano (KEDCO) domin samar da lantarki ga yankuna 100 da ba su da ita a jihohin Kano, Katsina da Jigawa.