✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu gasar shan kwaya a bikin aure sun shiga hannun NDLEA a Katsina

NDLEA ta cafke matashi da miyagun kwayoyi 50,000 da allurai 6,000 zai kai Kano; da wasu mutum 25 suna gasar shan miyagun kwayoyi a bikin…

Wasu masu gasar ’yar-kuren shan miyagun kwayoyi a bikin daurin aure a Jihar Katsina sun fada hannun hukumar yaki da miyagun kwayoyi (NDLEA).

Mutum 25 ne jami’an NDLEA suka cafke a yayin da suke tsaka da gasar shan miyagun kwayoyin a wani shagalin kafin daurin aure a unguwar Shola a Katsina.

Kakakin NDLEA Femi Babafemi ya ce a yayin samamen da aka cafke mutanen, an same su da kwayoyi da suke cakudawa a cikin wani bokiti suna sha.

“Duk da cewa angon da ya shirya gasar shan miyagun kwayoyi tare da abokansa ba ya wurin a lokacin, daga baya mun kamo shi,” in ji Babafemi.

Ya ce hukumar ta kama wani dan shekara 29 a Abuja dauke da tramadol kwaya 49,000 da alluran pentacozin 6,000, wadanda ya ce zai kai wa masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida  ba ne a yankin Doguwa a Jihar Kano.

A Jihar Borno kuma an kama wasu matasa uku da kwayar tramadol 81,975, biyu daga cikinsu a jihar, na ukun kuma sojoji suka kama shi a garin Mubi, Jihar Adamawa.

Hukumar ta kuma wata mace da maza biyu, har da dan kasar Jamhuriyar Nijar a wurare daban-daban a Jihar Kaduna dauke tabar wiwi mai nauyin kilo 81.