✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kamfani ya ba dan Shugaban DSS kyautar gidan N90m a Abuja

Gidan dai mai dakuna biyar yana unguwar Apo ne Babban Birnin Tarayya Abuja.

Wani kamfanin dillancin gidaje mai suna BSTAN ya bai wa dan shugaban hukumar tsaron farin kaya ta DSS, Yusuf Magaji Bichi, wato Abba Bichi kyautar gidan Naira miliyan 90 a Abuja.

Gidan dai mai dakuna biyar yana rukunin gidaje na Hiltop Estate ne a unguwar Apo da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.

Shugaban kamfanin, Injiniya Becky Olubukola ce ta sanar da haka ranar Alhamis, lokacin da ake kaddamar da Abban a matsayin Jakadan Matasa na rukunin gidajen Home Titan Network wanda daya ne daga cikin rukunin gidajen da kamfanin ke samarwa.

Shugaban ta kara da cewa irin kwazo da kokarni da matsahin yake bayarwa domin cigaban kamfanin ne ya sa suka ga cancantar yi masa kyautar.

Da yake jawabin godiya Abba Bichi ya bayyana godiyarsa ga kamfanin da kuma yan uwa da abokanan arziki da suke tallafa masa a ko yaushe.

A farkon watan nan dai sunan Abba ya karade gari, musamman a shafukan sada zumunta na zamani, bayan ya bayyana attajirin nan da Hukumar Yaki da Rahsawa ta EFCC ta kama, Obi Cubana, a matsayin mutumin kirki.