Yayin da ake tsaka da muhawara a kan matsalar fyade a ‘yan kwanakin nan, Karamar Ministar Babban Birnin Tarayya Abuja, Ramatu Tijjani ta bukaci a dandake duk wanda aka samu da laifin.
Yin hakan zai zama izina ga sauran jama’a, a cewar ministar wadda ta ce tuni Hukumar Birnin Tarayyar ta fara aiki kafada da kafada da masu ruwa da tsaki a harkar wajen ganin an yi wa tufkar hanci.
Ramatu Tijjani ta ce Hukumar Birnin ta fara hadin gwiwa da hukumomin tsaro da Hukumar Yaki da Safarar Dan Adam ta Kasa (NAPTIP) don tabbatar da hukunta duk wanda aka tabbatar ya aikata fyade.
“Za mu shigo da duk masu ruwa da tsaki a wannan yankin don yaki da matsalar fyade.
“Yanzu haka muna nan muna neman wani da ake zargi da aikata laifin ruwa a jallo kuma za mu damke shi a karshe Insha Allahu”, inji ministar ta bakin hadiminta ta bangaren yada labarai, Austin Elemue.
- Majalisar Tarayya ta ki yarda a dandake masu fyade
- Fyade: Kotu ta tsare dan shekara 57 da ya lalata yarinya
Ramatu ta kuma ce, “Gaskiya muna neman wani tsatstsauran hukunci a kan irin wadannan mutanen, dauri kadai ba zai wadatar ba, amma idan aka dandake su ina ganin hakan zai kawo maslaha.
“Idan muka ce za mu kashe su, to da zarar sun mutu shi ke nan, amma idan aka dandake su za su yi mutuwar tsaye, ga su da rai amma ba abin da za su iya tsinanawa”.
Ministar ta yi kiran ne lokacin da take raba kayan tallafi ga reshen birnin na kungiyoyin mata, Kungiyar Kwadago ta Kasa da kuma Kungiyar Masu Horas da ‘Yan Wasan kwallon Kafa a karshen makon nan.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake kira kan daukar hukunci mai tsanani kan masu dabi’ar lalata ‘ya’ya mata ta hanyar yi musu fyade ba, matsalar da a ‘yan kwanakin nan ke neman zama ruwan dare a Najeriya.