Tawagar Indomitable Lions ta kasar Kamaru ta kai zagayen daf da na karshe wato Semi-finals a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ke wakana a kasar.
Kamaru wadda ita ce mai masauki baki a gasar ta cimma wannan matsayi ne bayan da ta doke Gambia da ci 2-0 a Yammacin ranar Asabar.
- Har yanzu babu wani batu kan ’yan matan Chibok 110 da aka sace
- 2023: An nada tsohon Mataimakin Gwamnan Kano shugaban yakin neman zaben Osinbajo
Dan wasan gaban Kamaru Toko Ekambi ne ya zura kwallayensa biyu a ragar Gambia cikin tazarar mintina bakwai bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a filin wasan Japoma da ke birnin Douala.
Ita ma Burkina Faso ta bi sahun Kamaru, bayan doke Tunisia da ci 1-0, ta hannun dan wasanta Dango Ouattara gab da za a tafi hutun rabin lokaci.
Burkina Faso ta samu wannan nasara duk da cewa alkalin wasan ya daga wa Dango Ouattara katin sallama a minti na 82 kan ketar mahangurba da ya yi wa mai tsaron bayan Tunisia, Ali Maaloul.
Hakan ya sa Burkina Faso ta karasa wasan a daddafe da ’yan kwallo goma cikin mintina goma da suka rage a wasan da aka fafata a filin wasa na Garoua.
A yau Lahadi ce kuma tawagar kasar Masar za ta kara da Morocco, yayin da Senegal za ta fita kwanta-da-kwarkwata a karawar da za ta yi da tawagar Equatorial Guinea a zagayen kwata final na gasar ta AFCON.