Hassan Giggs mai shiryawa ne, daukar hoto kuma mai bada umarni a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood. Shi ne shugaban kamfanin shirya fina-finai na Giggs International dake jihar Kano.
An haifi Hassan Giggs a Kano, kuma ya fara koyon harkar daukan hoto tun yana karami a wajen mahaifinsa.
- Daga Jangebe ba za a sake sace dalibai a Najeriya ba – Buhari
- Ranar Talata za a kawo rigakakin COVID-19 kusan miliyan 4 Najeriya
- Ganduje ya ba mutumin da ya rasa iyalai 7 a gobara tallafin N3m
Har wa yau, Giggs ya halarci Los Angeles Center Studio dake birnin California a kasar Amurka da makarantar harkar fina-finai ta Jimark Film Institute dake jihar Legas, inda ya samu horo.
A shekara ta 2016 an zabi Hassan Giggs don zama daya daga cikin alkalan bikin bada kambu na African Magic Viewer’s Choice Award (AMVCA). Giggs ya shirya fina-finai da dama daga ciki akwai su Macijiya, Indon Kauye, Bayajidda, Sadauki da sauransu.
Daraktan nan ba da jimawa ba zai fara aikin sabon fim dinsa mai suna ‘Tsangayar Asali’. Fim ne da zai mayar da hankali kana bin da ya shafi almajiranci a shekaru 100 da suka shude.
Yayin tattaunawarmu da shi ta kafar sadarwa ta Instagram live, Giggs ya bayyana yadda satar fasaha ta jawo Kannywood mummunar asara a shekarun da suka gabata.
Aminiya: Matarka ita ce mace ta farko da ta fara bada umarni a fina-finan Kannywood, shin kai ne ka ja ra’ayinta ko yaya abun yake?
Giggs: Da farko dai na hadu da matata a masana’antar Kannywood, kuma tun a wancan lokaci ta nuna sha’awarta na zama mai shiryawa ko kuma bada umarni. A hankali na fara fita da ita wajen daukar shirin fina-finai musamman nawa na kaina. Daga baya kuma ta fara aiki dani a matsayin mataimakiyar mai bada umarni da kuma manajan shiri.
To, a haka ne ta samu gogewa sannan taje ta yi wasu kwas a kan harkar fina-finai wanda daga nan kuma ta fara bada umarnin fina-finai nata na kanta.
Aminiya: Kana yin hadin gwiwa da Nollywood wajen shirya fim dinka?
Giggs: Tabbas ina yi, misali akwai wani fim dana shirya na kuma gabatar mai suna ‘Hassana da Hussaina’ wanda a cikinsa na gayyato jarumai daga Nollywood da kuma Kannywood da dama. A Arewa muna da labarai masu kyau da birgewa, don haka lokuta da dama mukan tattauna tsakanin masana’antun biyu, don samun alfanu a tsakaninmu.
Aminiya: Wane albishir zamu samu daga Kannywood?
Giggs: Cikin ikon Allah nan ba da jimawa ba za a samu hadin gwiwa tsakanin Hollywood da Kannywood.
Aminiya: Za ka iya mana Karin bayana kan sabon fim dinka ‘Tsangayar Asali’?
Giggs: Tsangayar Asali fim ne da aka shirya shi kan yadda mutane ke yi wa abin da ya shafi Almajiri ko Almajiranci gurguwar fahimta. Mun shirya fim din ne, inda muka waiwayi shekaru 100 kan yadda ake Almajiranci a Arewacin Najeriya da ma wasu kasashe. Muna so ne mu nuna wani bangare mai nagarta game da Almajiranci.
Aminiya: Ko wannan dalilin ne yasa Gwamnatin Jihar Kano ta dauki nauyin fim din?
Giggs: Haka ne, amma fim din hadin gwiwa ne tsakanin kamfanin KDC Foundation da kuma Motion Pictures. Lokacin da gwamnan Kano ya ga wani bangare na fim din sai nuna sha’awarsa na bada tasa gudunmawar. Saboda ita ma gwamnatin Kano na da ra’ayi iri daya da wanda suka shirya fim din, sannan kuma a gidan gwamnatin Kano aka fara haska shi.
Aminiya: Daya daga cikin mabiyanka ya ce me yasa yawancin fina-finan Hausa suka fi mayar da hankali kan soyayya?
Giggs: Ina tunanin wannan nada nasaba ko tasirin kallon fina-finan Indiya da wasunmu key i, ba ma iya masu shirya fim ba, su kansu masu kallo sun fi son a shirya musu fim kan soyayya fiye da wani nau’in fim na daban.
Aminiya: Wane fim ne bakandamiyarka daga cikin wanda ka bada umarni?
Giggs: Fina-finan dana fi so akwai; Macijiya, Hindu, Sadauki da kuma Tsangayar Asali.
Aminiya: Wane kalubale masana’antarku ta shirya fina-finai ke fuskanta?
Giggs: Babbar matsalar da masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood ke fuskanta ita ce satar fasaha, saboda akwai masu sauki fim da zarar an sake shi a kasuwa, zasu ke turawa mutane ba tare da izinin mai fim ba. Hakan na kawo mana koma baya, saboda masu zuba kudinsu sun fara ja baya saboda gudun asara.
Kazalika, Sinimomi da gidajen Talabijin ma na daga cikin matsalar da muek fuskanta a yanzu, saboda ba mu da su yawa, hakan yana takaita mana inda ake haska fina-finanmu.
Aminiya: Nan da shekaru biyar wane mataki kake ganin Kannywood zata kai?
Giggs: Kannywood ta zata zama babbar masana’antar shirya fina-finai a Afrika ba wai iya Najeriya ba, saboda muna da nagartattun labarai, da wuraren daukar shiri masu yayin shirya fim.
Aminiya: Da akwai wani abu da zaka sanar damu game da Kannywood wanda bamu tambaya ba?
Giggs: Muna da jarumai masu kwararru, masu bada labari, masu shiryawa da bada umarni kwararru.