Daga Ustaz Aliyu Muhammad Sa’idu Gamawa
Matasan farko sun fahimci wannan koyarwar, sun yi imani kuma sun yi aiki tukuru; matasan yanzu sun tsaya a kan addu’a ne kawai ta “Allah Ya dora Musulunci a kan kafirci.” Kafirai kuma suna ta aikin ganin kafirci ya shiga gaban Musulunci ta hanyar raba Musulmi da turbar Musulunci da dora su a kan turbarsu; ga kadan daga cikin nau’o’in irin wannan kalubalen:
i. Shiga rabi-da-rabi ko ta kwaikwayon Turawa: Matasa Musulmi a yau sun fi jin dadin saka tufafi ba tare da hula ba, koda kuwa za su shiga sahun gaba a masallaci ko makarantar koyon darasin Musulunci, ko zuwa jana’iza, ko dawafi yayin aikin Hajji da makamantansu; kuma ba sa jin komai game da hakan. Wani lokaci ma su yi shigar da za su sabule wando, su take kafarsa, wai nan “kama kasa” a Ingilishi “earth down.” Matasa mata sun fi kwatanta shigar Musulunci a mafi yawan lokaci, saboda saka hijabi, wanda makarantun Islamiyya suka raya; amma su ma ana samun masu son su yi shiga irin ta Amurkawa, wajen bayyana surar jiki koda kuwa a wurin ibada ne; alhali masu hankali a Turai suna kishin mata Musulmi saboda alfarmar hijabi.
ii. Sai burin tara dukiya mai yawa, wani lokacin ko ta halin kaka.
iii. Ga gudun daukar nauyin ’yan uwa; matasa sun fi son su zauna nesa da dangi da iyaye; makwabci ya dade bai gaisa da makwabcinsa ba.
ib. Babban kalubale da watakila ya fi kowanne shi ne na raba addini da rayuwa, musamman a bangaren siyasa da shugabanci. Illolin raba siyasa ko shugabanci da addini suna da yawa a rayuwar Musulmi. Ga kadan daga ciki:
a) Imani shi ne ginshikin farko a rayuwar Musulmi; amma a kasahen Musulmi babu hukumar inganta imani, yayin da ake da hukumar cusa kishin kasa a zukata.
b) Sallah tana da muhimmanci a rayuwar Musulmi, amma da za a gayyaci shugabanni bude Masallacin Juma’a, lokacin ya ci karo da bude sabon ofishin jam’iyya, shugabanni za su je wurin bude ofishin ne, idan an ci sa’a su tura wakili wurin bude Masallacin Juma’a; alhali a wurin bude masallaci za a yi wa kasa addua’ar zaman lafiya, a roka wa shugabanni shiriya, amma a wurin bude ofishin jam’iyya za a yi ta yin ihu ne, a yi ta kirarin jam’iyya, watakila ma ’yan Jagaliya su duddura wa shugabanni ashar.
c) Azumi da ciyarwa cikin watan azumi suna da muhimmanci a Musulunci, amma kudin da ake warewa don ciyar da bakin gwamnati sun fi wadanda ake warewa don ciyar da mabukata a cikin watan Ramadan, wannan a ma inda ake da tsarin ciyarwar azumin ke nan.
d) Zakka ibada ce mai girma kuma hanya sahihiya ta kawar da talauci a cikin al’umma, kamar yadda binciken ilimi ya tabbatar, amma Hukumar Zakka a inda ake da ita, ba ta samun gatan hukumar tara haraji, duk da cewa Bature ya kirkiro ta ce da nufin cin zali da talauta al’umma.
e) Aikin Hajji da hukumar da take kula da shi, ba sa samun kudin da ake ware wa kwallon kafa da hukumar wasanni. A dalilin haka, idan ’yan kwallo za su fita waje, gwamnati ce take daukar nauyinsu, ta sama musu masaukin da ya fi wanda ake sama wa alhazai, ta ba su abincin da ya fi wanda ake ba alhazai, a samar musu motocin da suka fi na alhazai, idan sun dawo manyan jami’an gwamnati su tarbe su, su shirya musu walimar girmamawa yayin da ba wanda yake taren alhazai sai jami’an tsaro da wani lokacin suke karbe canjin da alhazan suka zo da shi.
f) Da ’yan musabakar Alkur’ani za su dawo sun ciyo lambar girma daga wata kasar, ’yan bal su dawo sun ciyo lamba a wata kasar, manyan jami’an gwamnati za su tarbi ’yan bal ne, su tura kanana wajen tarben ’yan musabaka; haka misalin yake da za ka hada ’yan fim da alhazai ko ’yan musabaka.
g) Makarantun boko sun fi gata a kan makarantun addini; akwai hukumar kula da ilimin firamare da ta kula da ilimin sakandare da ta kula da ilimin boko mai zurfi da ta kula da ilimin boko gaba daya. Ga kuma jami’o’i na karatun boko; amma babu hukumar kula da karatun allo ko na Islamiyya ko na zaure, ballantana a samu jami’ar ilimin addinin Musulunci. Hasali babu kwamitin kula da ilimin addini a Majalisar Tarayya; kwamitocin kula da addini a majilisun jihohin da ake da su, su ne ’yan autan kwamitoci.
h) Da a ce kowane mataki na ilimin addini za a samar masa da ma’aikata da kudade da sai a koyar da duk fannin ilimin zamani da Larabci; da kuwa an samu duk yawan likitocin da ake bukata da injiniyoyi da manoma da makiyaya da ’yan kasuwancin zamani da komai. Da kuwa sai a nemi almajirai a rasa, a nemi ’yan kwaya a rasa, a hutar da jami’an tsaro, a hutar da alkalai, a kau da cinkoson kurkuku, a raya kasa, a samar da aikin yi, a ji dadin mulki, kuma a samu yardar Allah. Ina matasa masu rike da madafan iko? kalubalenku! Tuni dai su Turawa suka dawo daga rakiyar raba addini da siyasa.
Matsalar rarrabuwa a addinance da siyasance: Hadisi ya ce mana kafirci addini ne guda daya; aya ta ce mana kafirai duk inda suke masu hada kai ne da jibintar juna, matukar Musulmi ba su zamo kamar haka ba, to, fitina da barna mai yawa za su kasance a bayan kasa. Amma mu an ce mana sai mun rarrabu jam’iyyu daban-daban sannan dimokuradiyyarmu za ta yi kyau; sai ga shi a cikin jam’iyya daya ma mun rabu gida-gida, a kowane gida mun rabu daki-daki, a kowane daki, shimfida-shimfida. Aka ce sai mun yi hamayya a zabe sannan zaben zai yi inganci; mu kuma sai muka maida abin adawa, alhali Allah Ya ce Shaidan ne kawai abokin adawarmu. Haka irin wannan rarrabuwar take a akidarmu; gyara wannan hali yana nan yana fuskantar matasa Musulmi a matsayin babban kalubale!
Shawarwari:
1. Ilimi: shi ne farkon abin da zai gyara al’amura. Don haka sai a dage wajen nemansa da yin aiki da shi.
2. Hadin kai: matasa su fara tunanin yin “merger” (wato hadaka) ta kungiyoyin addini da ake da su; a samu kadan masu kwari, masu nagarta, wadanda za su iya tsinana wani abu. kungiyar Jama’a Islami ta Indonesiya ta isa misali: a fannin ilimi, ta samarwa kasar Jami’a 400; a fannin lafiya tana da asibitoci a loko da sakon kasar; ita take tsara aikin Hajji ga mafi yawan ’yan kasar – ta yi musu adashin gata, ta hayi jiragen sama, ta tanadi masaukai da motoci da abinci. Don haka akwai bukatar samarwa da Musulmin Najeriya irin wannan kungiyar;
3. Matasa su rika daukar wata koyarwa ta Musulunci guda daya su dabbakata a shekara; misali: gaskiya, kula da lokaci, cika alkawari, tsabta, bin ka’ida, Sallah a jam’i, ko saka hula; bayan shekara, sai a sake daukar wani; kafin shekara goma sai an kayar da duk matsalolin da suke damunmu, kamar yadda ya faru a kasashe da dama;
4. Riko da sana’a ko yaya take;
5. Zaben mutane nagari a kowane matakin wakilci ko shugabanci.
Kammalawa
Malam Sa’adu Zungur ya fadi a wasu baitocinsa cewa:
Mu dai aikinmu fada muku,
Ko ku karba ko ku yi dariya,
Dariyarku ta zam kuka gaba,
Da nadamar mai kin gaskiya.
Allah Ta’ala Ya agaza mana, Ya ba mu ikon aiki da gaskiya, Ya kare mu da lafiya da imani.
Ustaz Aliyu Muhammad Sa’idu Gamawa
karamar Hukumar Gamawa Jihar Bauchi
08035829071