Bincike ya nuna cewa dubban mata ne a fadin kasar nan suke fama da lalurar yoyon fitsari.
Cutar na haifar da fitar fitsari ba tare da tsayawa ba, lamarin da ke sa masu ita shiga halin damuwa.
- Tinubu ba shi da lokacin zuwa tarukan muhawara –APC
- NAJERIYA A YAU: Yadda Soludo Ke Gyaran Tarbiyya A Anambra
Binciken da aka gudanar a fannin kiwon lafiya ya nuna cewa a mafi yawan lokuta cutar yoyon fitsari tana samuwa ne a dalilin doguwar nakuda da yin tiyata ga mata da kuma wasu abubuwa da suka shafi al’ada.