Asususn Tallafawa Ilimi da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya tabbatar da rasuwar mutum 122 daga cikin 1,387 da suka kamu da cutar mashako a jihohi 27 a Najeriya.
Wakiliyar ofishin Najeriya na UNICEF, Mis Cristian Munduate, ta ce hakan ya faru ne a watani bakwai da suka gabata, inda mutum 3,850 suka nuna alamun kamuwa da cutar, wadda ta addabar kananan yara.
- NAJERIYA A YAU: Makomar Jam’iyyar APC Bayan Naɗin Ganduje
- ’Yan kwadago sun yi barazanar sake komawa zanga-zanga
Wata takarda da ta aike wa Aminiya, Mis Cristian Munduate, ta ce kididdigar mace-macen ta nuna mutum takwas ne suka rasu a cikin kowane mutum dari da suka kamu da cutar.
Mis Cristian Munduate, ta ce akasarin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar ƙananan yara ‘yan kasa da shekaru 2 zuwa 14 ne.
Jami’ar ta ce, Kano da Yobe da Katsina da Legas da Abuja da Sakkwato da kuma jihar Zamfara, su jihoihn ke da cutar ta fi kamari da kimanin mutum 9 a cikin duk mutum 10 da suka kamu da cutar.
Game da kokarin da UNICEF ke yi na ganin an shawo kan cutar da ta barke a wasu Jihohi 27 na Najeriya, Mis Cristian ta ce “Abu ne mai matuƙar sosa rai jin cewa kashi ishirin da biyu cikin ɗari ne kawai aka yi wa allurar rigakafin da ake yi wa ƙananan yara.
“Wadanda suka kamu da cutar mashaƙon har suka mutu suna cikin waɗanda ba a yi wa rigakafin ko sau ɗaya ba” inji ta.
UNICEF ya ce idan ana bukatar sanar da wadanda ba a iya kaiwa gare su ba hakan ba wani abu ne mai wuya, saboda UNICEF da haɗin gwiwar Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta (NCDC) da jihohin da abin ya shafa da kuma hukumar kula da lafiya matakin farko ta Ƙasa (NPHCDA) don ganin an yi tsari na tabbatar da ɗaukin da za a kai.
Daga nan sai tace UNICEF ta jajirce wajen faɗaɗa ba da tallafin a nau’ika daban-daban da suka haɗa da tsarawa da aiwatar da tallafawa wajen sanar da bayanai game da afkuwar haɗura.