Cutar Kwalara ta kashe akalla mutane hudu tare da kwantar da wasu biyu a garin Yadin Buni, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Gujba ta Jihar Yobe.
Ana zargin bullar cutar a kauyukan Jangalawaje da Tadangara da ke a karamar hukumar.
Wata majiya daga Hukumar Kula da Lafiya a Matakin farko, a karamar hukumar ta ce, “Akalla mutane 45 aka samu da alamomin cutar kwalara, daga cikinsu hudu sun mutu, an kwantar da wasu biyu a PHC Buni Yadi.”
Bayan wata mummunar ambaliyar ruwa a sassan jihar, kwararru a fannin lafiya sun jaddada buƙatar a rika tsaftace muhalli domin daƙile barkewar cututtuka kamar kwalara.
Wata majiyar kiwon lafiya a karamar hukumar ta ce, tunin wata tawagar agajin gaggawa da hadin gwiwar bayan abokan hulɗa kamar WHO, UNICEF, da CDC sun ziyarci yankin don kai daukin gaggawa da wayar da kan jama’a dangane da tsaftace muhalli da dangoginsa.
“An yi aikin wayar da kan jama’a kan tsaftar ruwa, tsaftar abinci, tsaftar muhalli, a yankuan da abin ya shafa.
“Ya zuwa yanzu an ba da magunguna ga majinyatan da abin ya shafa a yankunan biyu” inji majiyar.
Aminiya ta tattaro cewa hukumar lafiya ta duniya ta umurci jami’an lafiya a karamar hukumar da su tattara samfurin ruwa a yankunan domin gudanar da bincike.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Muhammad Lawan Gana, ya ce “muna sane da cutar kwalara a wata unguwa da aka samu ambaliyar ruwa a Gujba a makon jiya.
“Tuni an shawo kan lamarin, kuma ba a samu sabbin masu kamuwa da cutar ba, gudawa cuta ce da ta zama ruwan dare musamman a wuraren da ake samun ambaliyar.
“Kungiyar kiwon lafiya da abokan hulɗa suna ta kokarin kawo daukin gaggawa da zimmar shawo wannan annoba,” in ji Dr Gana.