✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kalli yadda Buhari ya yi Sallar Idi a gida tare da iyalansa

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Sallar Idi a gida tare da iyalansa da wasu jami’an fadar gwamnati ta Aso Rock Villa. Da ma dai shugaban…

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Sallar Idi a gida tare da iyalansa da wasu jami’an fadar gwamnati ta Aso Rock Villa.

Da ma dai shugaban kasar, ta bakin mai ba shi shawara a kan al’amuran yada labarai Malam Garba Shehu, ya ce bisa shawarwari da ka’idojin kare kai daga cutar coronavirus da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta NCDC da Kwamitin Shugaban Kasa Mai Yaki da COVID-19 suka fitar, a gida zai yi sallar.

Sannan ya ce ba zai karbi gaisuwar Sallah kamar yadda ya saba ba.