✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kakar Darakta Falalu Dorayi ta rasu

Kakar daraktan ta rasu tana da shekara 110 a duniya.

Kakar Darakta a masana’antar Kannywood, Falalu A. Dorayi, Hajiya Amina Nene Yakumbo ta rasu a safiyar ranar Talata.

Daraktan ne da kansa ya sanar da rasuwar kakar tasa a shafukansa na kafafen sada zumunta, inda ya ce “Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un. Kakata Hajiya Amina (Nene Yakumbo, Yadikko) ta rasu.

“Za a yi jana’izarta da misalin karfe 12 a Gidan Makers da ke unguwar Ja’en Dorayi. Allah ya yafe mata kurakurenta,” kamar yadda ya wallafa.

Rahotanni sun bayyana cewar Hajiya Amina ta rasu tana da shekara 110.

Tuni aka shiga yi wa daraktan gaisuwa da jaje game da rasuwar kakar tasa.