Mai magana da yawun kungiyar kabilar Yarabawa ta Afenifere, Yinka Odumakin ya rasu bayan fama da cutar COVID-19.
Iyalan Yinka Odumakin sun ta shaida wa Aminiya cewa ya mutu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas (LASUTH), inda aka kai shi, bayan yanayin rashin lafiyar tasa ya tabarbare.
- Tafsirin Ramadan: Izala ta tura malamai 500 zuwa kasashe
- An fara yi wa maniyyata aikin Hajji rigakafin COVID-19
- Gobara a babbar kasuwar kayan mota a Ibadan
Odumakin ya jigo ne a hadaddiyar kungiyar nan ta NADECO wacce ta yaki gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha bayan soke zaben 12 ga Yuni, 1993.
Ya kuma kasance daya daga cikin masu magana da yawun Kungiyar Shugabannin Kudu da Arewa ta Tsakiya (SMBLF), mai wakiltar kabilun Kudu-maso-Yamma, Kudu-Kudu, Kudu-maso-Gabas da Arewa ta Tsakiya.
Marigayi Odumakin ya kuma yi kaurin suna wajen sukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, da zargin ta da nuna bangaranci da fifiko wajen bayar da mukamai.
Muryarsa kuma tana da karfi sosai wajen caccakar ayyukan wasu masu kisan kai a yankin Yarbawa.
A kwanan nan ya gargadi Gwamnatin Tarayya cewa kar ta tsare Sunday Igboho wanda ya ba da sanarwar cewa Fulani makiyaya su tashi daga Ibarapa, Jihar Oyo sannan kuma ya kori Sarkin Fulanin a Igangan.
Marigayin shi ne mai magana da yawun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a zamanin rusasshiyar CPC, jam’iyyar da Buhari ya tsaya takara amma ta fadi a zaben 2011.