Shugaba Muhammadu Buhari na jagorantar zaman Majalisar Tsaro ta Kasa, gabanin tafiyarsa zuwa birnin London na kasar Birtaniya domin ganin likita.
Bayan taron na ranar Talata ne Buhari zai kama hanyarsa ta zuwa London domin duba lafiyarsa sannan ya dawo a cikin mako na biyu na watan Afrilu.
- Buhari ya saki kudi kawai talaka ya ji dadi —Tinubu
- Fada a jirgi: Okorocha bai ga komai ba tukuna —Basarake
- Limami ne ya sa na kashe mahaifiyata
- ‘Yadda na gudu a hannun masu garkuwar da suka kama mu’
Taron da ke gudana a zauren Majalisar Zartarwar ta Kasa ta samu halarcin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo; Mashawarcin Shugaban Kasa Kan Tsaro, Babagana Monguno da kuma Ministan Tsaro, Bashi Magashi.
Daukacin Manyan Hafsoshin Tsaro da Shugabannin ’Yan Sanda, Hukumar tsaro ta DSS, da Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA) na halartar zaman.
Sauran mahalarta su hada da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gamba; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha.