’Yan bindiga sun harbe Magajin Garin Idasu a ke Karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna, Malam Magaji Ibrahim.
Kisan nasa ne zuwa ne kasa da kwana daya bayan ’yan bindigar sun hallaka mutum 38 a sassa daban-daban na Jihar, ciki har da Karamar Hukumar.
- Sanata ya raba wa ’yan mazabarsa motoci 50 da babura 500 a Gombe
- Kani ga tsohon Gwamnan Kano, Kwankwaso, ya rasu
Daya daga cikin shugabannin matasa a kauyen Rahiya, Ridwan Abdullahi, ya shaida wa Aminiya cewa kusan kaso 70 cikin 100 na mutanen kauyen tuni suka yi gudun hijira zuwa wasu yankunan Kananan Hukumomin Zariya da Giwa, don neman mafaka.
Rahotanni sun ce an kashe shi ne yayin wani hari da suka kai a yankin ranar Lahadi.
Wani mazaunin yankin, Sharehu Idasu, ya ce an harbe basaraken ne lokacin da ya fito daga gidansa yana neman taimako, yayin da ’yan bindigar suka mamaye yankin.
Ya ce, “Maharan da suka zo yankin da daren ranar Lahadi ne suka harbe shi bayan sun mamayen yankin Idasu, sannan suka sace babura. Ya fito ne yana neman taimako, inda suka harbe shi nan take.”
Sharehu ya ce tuni aka yi wa basaraken jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
“Sama da kaso 70 cikin 100 na mutanenmu sun gudu wajen ’yan uwansu a Zariya da Giwa bayan mummunan harin. An kashe mutum 23 a kauyen Rahiya kawai, 21 daga cikinsu duka masu aure ne, biyu ne kawai basu da aure,” inji shi.
Aminiya ta rawaito yadda a ranar Litinin maharan suka mamaye garuruwan Kauran Fawa da Marke da Rahiya, dukkansu a gundumar in Idasu ta Karamar Hukumar Giwa.
Kwamishinan Tsaro Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce jimlar mutum 38 ne aka kashe a sassa daban-daban na Jihar.
Sai dai duk kokarin wakilinmu na jin ta bakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ya ci tura, saboda Kakakinta, ASP Mohammed Jalige, bai samu damar daga waya ba.