✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kaduna ta fadada dokar kullen Zangon Kataf da Kauru

Gwamnatin jihar Kaduna ta fadada dokar hana fita na awa 24 da ta sanya zuwa fadin kananan hukumomin Zangon Kataf da Kauru. Jihar Kaduna ta…

Gwamnatin jihar Kaduna ta fadada dokar hana fita na awa 24 da ta sanya zuwa fadin kananan hukumomin Zangon Kataf da Kauru.

Jihar Kaduna ta fara sanya dokar ne biyo bayan tashin hankalin da ya so afkuwa a yankunan biyu da suka kunshi Masarautun Atyap da Chawai.

Dokar, wadda ta shafi masarautun biyu, yanzu za ta hada da dukkannin masarautun da ke fadin kananan hukumomin biyu.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Aruwan, ya bayyana cewa jami’an tsaro na kokarin shawo kan lamarin da ke neman kazancewa kan rikicin filayen noma.

“Kara fadada dokar hana fita zuwa sassan Kananan Hukumomin na daga cikin matakan da muka yi amanna za su taimaka wajen dawo da zaman lafiya a yankin.” Inji sanarwar.