A yayin da Gwamna Uba Sani ya cika kwana 10 a kan mulkin Jihar Kaduna bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu, 2023; Ga wasu muhimman abubuwa da ya yi:
Nadin mukamai
Tun kwanaki biyu kafin rantsar da Uba Sani ya nada Muhammad Shehu Lawal, mashawarcin tsohon gwamna Nasir El-Rufai, a matsayin kakakinsa.
- NYSC ta tura wa mai yi wa kasa hidima dubu 330 bisa kuskure
- Kotu ta daure DJn da ya hana Islamiyya sakat da kida a Kano
Kwanaki biyu bayan rantsarwa kuma ya ayyana mutum 27 da za su kasance mashawartansa, cikinsu har da wadanda suka yi aiki a Gwamnatin El-Rufai.
Sakataren gwamnatin El-Rufai, Balarabe Abbas Lawal, zai ci gaba da rike da mukamin; mashawarcin El-Rufai, Hafiz Bayero ya zama babban mai ba shi shawara; shi kuma tsohon Kwamishinan Ilimi, Muhammad Shehu Makarfi, aka nada shi mashawarci ga sabuwar gwamnatin.
Ganawa da jami’an tsaro
A makon jiya Gwamna Uba Sani ya yi ganawa ta musamman da shugabannin hukumomin tsaron da ke jiha, inda a lokacin ganawar ya sha alwashin bai wa jami’an tsaro duk taimako da goyan bayan da suke bukata domin magance matsalar tsaro a jihar.
A cewarsa kare rayuka da dukiyoyin al’ummar ne gwamnatinsa za ta mayar da hankali a kai, don haka ya bukaci hadin kan jama’a ga jami’an tsaro domin samun nasara a yaki da bata-gari a jihar.
Kwamitin gyaran ma’aikatun gwamnati
Sanata Uba Sani ya kuma kafa kwamitin garanbawul ga ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar, wanda mataimakiyarsa, Hadiza Sabuwa Balarabe za ta shugabanta.
Gwamnan ya ba wa kwamitin da aka kafa a ranar 5 ga watan Mayu, 2023 wa’adin makonni biyu ya gabatar masa sakamakon bincikensa domin gani yadda hukumomin da ma’aikatu ke gudanar da ayyukansu.
Kwamitin ya kunshi manyan jami’an gidan gwamnati da shugaban ma’aikatan jihar da kuma masana.
Sulhu da kungiyar kuwadago
Bayan sa-toka-sa-katsi da aka shiga a Najeriya kan janye tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi, Gwamna Uba Sani, ya gana da kungiyar kwadago a Jihar Kaduna, don shawo kanta game shirinsu na shiga yajin aiki.
Ya shaida wa taron cewa Shugaba Tinubu ba shi da zabi illa janye tallafin saboda dama gwamnati mai barin gado ta cire shi a cikin kasafin kudin bana.
Don haka ya ga dacewar ya zauna da ’yan kwadago domin lalubo hanyar da za a sama wa talakawa mafita domin rage musu radadin tallafin da aka cire.
A karshe bangarorin sun amince su kafa kwamitin da zai fito da tsare-tsare da hanyoyin rage radadin janye tallafin.