Wannan ita ce fassarar hudubar da Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ba da umarnin a karanta ta a Juma’ar da ta gabata a fadin kasar nan:
Da Sunan Allah Mai rahama Mai jinkai.
Bayan haka, ’yan uwa Musulmi! Hakika muna cikin wata irin jarrabawa mai tsananin gaske a cikin wannan kasa tamu Najeriya; muna cikin jarrabawar rashin mulkin adalci daga wasu shugabanni, muna cikin jarrabawar fadace-fadace irin na kabilanci da addini, muna cikin jarrabawar ’yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane, muna cikin jarrabawar masu daukar makamai domin yakar hukuma. Hakika, wadannan bala’o’i da muka ambata sun yi sanadin tabarbarewar al’amura, sun yi sanadin yaduwar talauci da rashin aikin yi a tsakanin ’yan kasa, sannan sun yi sanadin kashe rayukan jama’a da yawa wadanda ba su ji ba, ba su gani ba. Fa’inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!
’Yan uwa Musulmi! Lallai duk da wannan hali da muke ciki na tabarbarewar lamura ba za mu fidda tsammanin kyautatuwar wadannan lamuran ba, ba za mu fidda tsammanin samun rahamar Allah da tausayinSa gare mu ba. Saboda Allah Madaukakin Sarki Ya ce a cikin Suratul Hijri aya ta 56: “Babu mai yanke tsammanin samun rahamar Ubangijinsa sai batattu.” Ya kuma ce a cikin Suratu Yusuf aya ta 87: “Lallai yadda lamarin yake, babu mai yanke tsammanin samun rahamar Allah sai mutane kafirai.” Ya kuma ce cikin Suratul A’arafi aya ta 156: “RahamaTa ta yalwaci dukkan komai, da sannu Zan rubuta ta ga wadannan da suke tsare dokokin Allah, kuma suke ba da zakka, wadanda suke imani da ayoyinMu.”
’Yan uwa Musulmi! Da ma ita rayuwar mutum haka take, wata rana cikin dadi, wata ranar kuwa cikin wahala, to amma su al’ummar Musulmi wadanda suka yi imani da Allah a matsayin Ubangijinsu, suka yi imani da Musulunci a matsayin addininsu, suka yi imani da Annabi Muhammad (SAW) a matsayin Annabinsu kuma Manzo zuwa gare su, lallai wadannan ba sa gushewa cikin alheri bayan alheri, matukar dai zukatansu na rataye da Ubangijinsu, suna kuma kaskantar da kai gare Shi suna kuma nuna naciya cikin rokonSa dare da rana.
’Yan uwa Musulmi! Lallai abu mafi alheri da al’ummar Musulmin Najeriya za su aikata domin samun kubuta daga bala’o’in da suke cikinsu a yanzu, shi ne muraja’ar kai (duba kawunansu) da kyautata ayyuka da fuskantar Allah Madaukakin Sarki cikin kaskantar da kai, da yawaita addu’a dare da rana. Domin ita addu’a wata babbar makami ne ga salihan bayi, a gaskiya ma addu’a ita ce ginshikin ibada. Abu Dawud a Hadisi na 1479 da Tirmizi a Hadisi na 2969 da Ibnu Majah a Hadisi na 3828, sun ruwaito da isnadi sahihi daga Nu’uman dan Bashir cewa: “Manzon Allah (Mai tsira da amincin Allah) ya ce: “Addu’a ita ce Ibada” daga nan sai ya karanta fadin Allah cikin Suratu Gafir aya ta 60: “Ubangijinku Ya ce ku roke Ni, Zan amsa muku, lallai wadanda suke nuna girman kai ga bauta miNi da sannu za su shiga Jahannama suna kaskantattu.”
Ya ku al’ummar Musulmi! Hakika ita addu’a tana da wasu ladubba, wanda duk ya kiyaye su, in sha Allahu za a amsa masa addu’arsa.
Ga mafiya muhimmanci daga wadannan ladubba:
Na daya: Yin addu’o’in cikin lokuta masu daraja, kamar Ranar Arafa, ko cikin watan Ramadan ko ranar Juma’a, ko sulusin karshe na dare, ko tsakanin kiran Salla da ikama da makamantansu.
Abu Dawuda ya ruwaito a Hadisi na 521 da Tirmizi a Hadisi na 212 da Ahmad a Hadisi na 22,174 da isnadi sahihi daga Anas dan Malik (RA) ya ce: “Manzon Allah (Mai tsira da amincin Allah) ya ce: “Ba a kin karbar addu’a a tsakanin kiran Salla da ikama.” Bukhari ya ruwaito a Hadisi na 935 da Muslim a Hadisi na 852 daga Abu Huraira ya ce: “Manzon Allah (Mai tsira da amincin Allah) ya ce: “Lallai akwai wata sa’a a ranar Juma’a, Musulmi ba zai roki Allah wani alheri a cikinta ba face sai Ya biya masa bukatarsa, wata sa’a ce mara yawa.” Har yanzu Bukhari ya ruwaito a Hadisi na 6321 da Muslim a Hadisi na 758 daga Abu Huraira ya ce: “Manzon Allah (Mai tsira da amincin Allah) ya ce: “Ubangijinmu Tabaraka wa Ta’ala Yana saukowa cikin ko wane dare a sulusin karshe na dare Yana cewa: “Wa ke kiraNa in amsa masa, wa ke rokoNa in ba shi, wa ke neman gafaraTa in gafarta masa?”
Na biyu: Yin addu’ar cikin wani hali na daraja da ake ciki, kamar lokacin saukar ruwan sama da lokacin da mai azumi yake yin buda baki da lokacin sujuda a cikin Sallah da lokacin da bawa ke cikin halin tafiya. Muslim ya ruwaito a Hadisi na 482 daga Abu Huraira ya ce: Annabi (Mai tsira da amincin Allah) ya ce: “Lokacin da bawa ke fin kusanci da Ubangijinsa shi ne lokacin da yake sujuda, saboda haka ku yawaita addu’a.” Abu Dawuda ya ruwaito a Hadisi na 1536 da Tirmizi a Hadisi na 1905 da Ibnu Majah a Hadisi na 3862 da Ahmad a Hadisi na 8375 da isnadi mai kyau daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Manzon Allah (Mai tsira da amincin Allah) ya ce: “Addu’o’i uku karbabbu ne ko shakka babu: addu’ar mahaifi da addu’ar matafiyi da addu’ar wanda aka zalunta.”
Na uku: Idan mutum zai yi addu’a ya fuskanci Alkiblah ya daga hannayensa ya sassauta muryarsa, ya kuma nisanci Saja’i. Allah na cewa cikin Bakara aya ta 186: “Idan bayiNa suka tambaye ka labariNa ka ce: “Lallai Ni kusa Nake, Ina kuma amsa kiran mai kira idan ya kira Ni, saboda haka su amsa miNi, su kuma yi imani da Ni, tsammanin za su shiriyu.” Kuma Ya ce a cikin Isra’i aya ta 110: “Kada ka bayyanar da addu’arka, kada kuma ka boye ta, ka rika yin ta tsaka-tsaki.” A Hadisi na 1737 cikin Buhari Abdullahi dan Abbas ya ce: “Ka dubi duk abin da yake na saja’i ne a cikin addu’a ka guje masa, saboda ni na lura cewa wannan shi ne abin da Manzon Allah da sahabbansa suke yi.”
Na hudu: Sanya ikhlaasi da nuna tsoron Allah cikin addu’ar da kuma sakankancewa cewa lallai Allah Mai karbar addu’ar bayinSa ne. Tirmizi ya ruwaito a Hadisi na 3479 da Ahmad a hadisi na 6617 da Hakim a Hadisi na 1817 da isnadi mai kyau daga Abu Huraira ya ce: Manzon Allah (Mai tsira da mincin Allah) ya ce: “Ku roki Allah kuna masu sakankancewa da samun ijaba, ku sani lallai Allah ba Ya amsar addu’a daga zuciyar gafalallai rafkananne.” Bukhari ya ruwaito a Hadisi na 6338 daga Anas dan Malik ya ce “Manzon Allah (Mai tsira da amincin Allah) ya ce: “Idan dayanku zai yi addu’a to ya yi ta da karfin gwiwa kada ya ce: Ya Allah in Ka so Ka ba ni; saboda babu mai iya tilasta Shi.”
Na biyar: Ya nuna naciya cikin addu’arsa, sannan kada ya nuna cewa me ya sa har yanzu ba a biya masa bukatarsa ba? Bukhari ya ruwaito a Hadisi na 6340 da Muslim a Hadisi na 2735 daga Abu Huraira ya ce: “Manzon Allah (Mai tsira da amincin Allah) ya ce: “Za a amsa wa dayanku addu’a matukar bai nuna gaggawa ba, ya rika cewa: “Na yi addu’a amma ba a amsa mini ba.”
Na shida: Ya bude addu’ar da rufe ta da ambaton Allah da kuma yi wa Annabi salati, daga nan sai ya gabatar da addu’arsa. Bukhari ya ruwaito a Hadisi na 1130 da Muslim a Hadisi na 769 daga Abdullahi dan Abbas ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya kasance in ya tashi sallar dare yana cewa: “Ya Allah! Godiya ta tabbata gare Ka, Kai ne hasken sammai da kasa, godiya ta tabbata gare Ka, Kai ne madogarar sammai da kasa, godiya ta tabbata gare Ka, Kai ne Ubangijin sammai da kasa da abin da ke cikinsu, Kai ne gaskiya, alkawarinKa gaskiya ne, zancenKa gaskiya ne, gamuwa da Kai gaskiya ne, Aljanna gaskiya ce, Wuta gaskiya ce, Sa’a gaskiya ce. Ya Allah gare Ka na mika wuya da Kai na yi imani da tawakkali, zuwa gare Ka na koma, saboda Kai nake husuma, wurinKa nake kai kara. Ka gafarta mini abin da na gabatar da abin da na jinkirta, da abin da na boye da abin da na bayyana. Kai ne Abin bautana, babu abin bauta bisa cancanta sai Kai.” Tirmizi ya ruwaito a Hadisi na 486 da isnadi mai kyau cewa Umar dan Khattab ya ce: “Lallai addu’a a dakace take tsakanin sama da kasa babu abin da ke kaiwa sama daga cikinta har sai ka yi salati ga annabinka tukun.”
Na bakwai: Tuba daga ayyukan zunubi da kuma maida duk kayan zalunci da ke hannunka da takaituwa da cin halal. Muslim ya ruwaito a Hadisi na1015 daga Abu Huraira ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ambaci labarin wani mutum da yake tsawaita tafiya gashi a cike da kura yana mika hannayensa zuwa sama yana cewa: “Ya Ubangiji! Ya Ubangiji!! Alhali abincinsa haram ne, abin shansa haram ne, tufarsa haram ce, kuma da haram aka ciyar da shi, ta yaya za a amsa masa?”
Ya Allah! Muna rokon Ka, Ka amsa mana addu’o’inmu, Ka dawo mana da zaman lafiya cikin kasarmu, Ka kyautata mana shugabanninmu, Ka sa albarkarKa ta game dukkan al’ummarmu.
Bayin Allah! Lallai Allah Yana umarni da adalaci da kyautatawa da ba ma’abucin zumunta hakkinsa, kuma Yana hani daga alfasha da abin ki da zalunci. Yana yi musu wa’azi tsammaninku kuna tunawa. Ina fadin wannan magana tawa ina mai neman gafarar Allah gare ni da ku daga dukkan zunubi, ku nemi gafararSa, lallai Shi Mai yawan gafar ne Mai jinkai