✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kada mu bai wa maƙiya gudunmawar lalata Kano — Sanusi II

Ya kamata mutanen Kano mu yi wa kan mu nasiha, mu daina faɗa wa tarkon maƙiyan Kano.

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga jama’a da kada su bari maƙiya su yi amfani da su wajen lalata Kano da Arewa da kuma Najeriya baki daya.

Sarkin ya yi kiran ne yayin da rahotanni ke cewa masu zanga-zangar sun fara kara fantsama titunan birnin na Kano, duk da dokar hana fita da aka sanya don dakatar da tashin hankalin da ya biyo bayan zanga-zangar a jiya Alhamis.

Aminiya ta ruwaito yadda wasu matasa masu zanga-zangar suka hadu a kan gadar da ke tsakanin Tudun Murtala da Tudun Wada, da ke Karamar Hukumar Nassarawa a jihar, da dama daga cikinsu suna dauke da kwalaye masu sakonnin bukatunsu.

Masu zanga-zangar sun fara haduwa ne bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da sassauta dokar hana zirga-zirgar domin bai wa jama’a damar zuwa sallar Juma’a.

A wani taron manema labarai da Sarkin ya yi a fadarsa da ke Gidan Rumfa, ya nuna damuwa sosai kan yadda aka barnata kayan jama’a da na gwamnati yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka soma a ranar da ta gabata.

Sarkin ya ce abin da ya faru ci baya ne ga jihar da Arewa da ma kasar gaba daya.

“Muna kira ga iyayen yara da shugabanni a unguwanni da ƙauyuka su ja kunnen matasa, su san cewa abubuwan nan da ake yi koma-bayanmu ne.

“Idan muka duba ginin Hukumar Sadarwa ta Nijeriya da masu zanga-zangar suka lalata, mu Kanawa mu ne muka yi asara domin an gina ta ne da nufin horas da matasa kan fasahar zamani.

“Ba a jima ba na yi magana da ministan sadarwa wanda ya tabbatar min cewa sun shirya zuwa kaddamar da hukumar a makon gobe tare da gwamna, amma yanzu an lalata wurin an wawushe kayan da ake ciki na miliyoyin naira.

“Waɗannan abubuwa da muke yi kanmu muke cuta. Ku duba sauran jihohin da aka yi wannan [zanga-zangar], mafi yawancin wuraren da aka yi ɓarna jihohin Arewa ne.

“Ya kamata mutanen Kano mu yi wa kanmu nasiha, mu daina faɗa wa tarkon maƙiyan Kano. Duk mutumin da ya zo da fitina garin nan ba shi ƙaunar wannan ƙasa.

“Ina kuma addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar wannan zanga-zanga sannan kuma Ya mayar da alheri ga wadanda aka yi wa barna da sace musu kaya. Ya kuma inganta lafiyar wadanda suka jikkata.

“Muna adduar Allah Ya ci gaba da dafa wa wadanda suke yi wa Kano fatan alheri. Muna kuma kara kiran al’umma da su zama jakadu na zaman lafiya a koda yaushe.”