Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce, ya bukaci al’ummar Najeriya su zabi ’yan takara bisa cancanta da kuma la’akari aikin da suka yi masu a zaben 2019 da ke tafe.
Shugaba Buhari wanda ya fadi haka a wata hira da ya yi da gidan rediyon Muryar Amurka, ya ce bai ga dalilin da zai sa Gwamnatin Tarayya za ta bai wa gwamnoni kudi domin gudanar da ayyuka, amma su gaza biyan albashi.
Ya ce yana mamakin yadda gwamnoni za su iya zuwa su kwanta su yi barci bayan sun san akwai mutanen da ke aikin gwamnati da ba su biya su albashinsu ba, kasancewar suna da iyalin da za su biya bukatunsu, da suka hada da biyan kudin makaranta da zuwa asibiti da sayen abinci.
Shugaba Buhari ya ce tsarin mulkin kasar nan ya bai wa gwamnonin ’yancin kashe kudin da suka samu ba tare da tsangwama ba, sai dai wannan ya zama damar da wadansu suke fakewa suna kin yi wa al’umma aiki. Saboda haka, ya shawarci talakawa su yi amfani da ’yancinsu na zabe su zabi wadanda suka san za su yi musu aiki.
Dangane da yaki da cin hanci da rashawa, Shugaba Buhari ya ce hanyar da yake bi a halin yanzu ita ce hanyar da tsarin dimokuradiyya ya amince da shi. Ya ce a baya ya dauki wani mataki na daban, amma kasancewar yanzu ana mulkin dimokuradiyya ne tilas ya bi tsarin. Sai dai ya ce duk da tsarin yana daukar lokaci, amma duk da haka, ana samun ci gaba.
Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi rawar gani a fannin wutar lantarki, domin ya ce akwai bambanci tsakanin yadda ake samun wutar lantarki yanzu da yadda take shekara hudu da suka gabata. Ya ce masu yin sana’o’i suna shaida ci gaban da aka samu a wannan fanni, wadanda a da suke amfani da janareta domin gudanar da sana’o’insu.
“Kokarin gwamnatin yanzu shi ne mai da hankali wajen neman hanyar samar da wuta da ke amfani da hasken rana domin magance matsalar fasa bututu da wadanda suke zaune a inda ake samar da iskar gas suke yi da kuma gudun fuskantar karancinsa,” inji shi.
Dangane da inganta harkokin noma, Shugaba Buhari ya ce a shekarar 2016 ya gayyaci Ministan Harkokin Noma da kuma Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya ce su nemi hanyar da za su bi wajen ba da bashi ga manoma cikin sauki domin tallafa wa masu karamin karfi ba tare da bin hanyoyin da aka saba bi ba, da suke da tsawo da kuma wahalarwa ga kananan manoman. Banda haka kuma ya ce an samar da takin zamani isasshe wanda ya taimaki manoman da suka amsa kira suka rungumi noma, abin da ya taimaka wajen bunkasa harkokin noma a kasar nan.