Kungiyar nan mai fafutukar kafa kasar Biyafara ta IPOB ta gargadi Jakadiyar Birtaniya a Najeriya, Catriona Laing, da ta soke ziyarar da ta shirya kai wa jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya.
Haramtacciyar kungiyar dai ta yi ikirarin bankado wata makarkashiyar da ake da ita ta hallaka ta a yankin yayin ziyarar.
A cewar IPOB, wacce ta ce ta sami wasu bayanan sirri daga sashen leken asirinta, inda ta ce an shirya yin hakan ne don a zargi kunguyar ta su da aikata hakan.
Daraktan Yada Labarai na kungiyar, Emma Powerful, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce, “Jakadiyar ta Birtaniya na da wata kiyayya da kafuwar kasar Biyafara, saboda haka ya zama wajibi duniya ta san halin da ake ciki, saboda muna mutunta rayuwar dan Adam.
“Muna kira ga Jakadiyar da ta soke ziyarar da ta shirya kai wa wasu sassa na Najeriya, musamman ma yankin kasar Biyafara, wanda ake kira da Kudu maso Gabas.
“Dalilinmu shi ne ba wata kumbiya-kumbiya, muna so ne mu ceci rayuwarta, duk da yake sam ba ta kaunar Biyafara, amma muna girmama rayuwar mutum,” inji sanarwar.