Taku: Amina Abdullahi.
Akwai wani rafi da ke cikin wani daji. A rafin akwai kifaye da dama a ciki domin mutane ba su san da wannan rafin ba. Kullum kifayen sai su yi ta shawagi.
A gefen rafin akwai wani Kada wanda a kullum sai ya ba su shawara a kan yadda za su rika tafiyartar da al’amurarsu amma kifayen ba su jin magana. Har suka rada wa Kadan ‘sarkin bada shawara’.
Ran nan sai wasu maharba sun fito daga yawon neman naman daji kawai sai suka hango rafi. Suka nufi rafi domin shan ruwa sai suka ga kifaye makil a ciki. Sai dayan ya ce sun yi nasara. dayan kuma yace su bari zuwa gobe sai su zo da kwandon kamun kifi.
Kada na jin haka sai ya shiga cikin ruwa ya ba kifaye shawarar yin hijira amma suka ki.
Washegari sai maharban suka dawo suka kwashe duk kifayen da ke cikin kogin. Daga nan kifaye suka yi nadama suka yi da-na-sanin da sun bi shawarar da kada ya ba su tun da farko.