Kocin kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 23 (U-23) Samson Siasia ya ce kada wanda ya zarge shi idan kungiyar ta kasa hayewa gasar Olamfik da zai gudana a Brazil a shekarar 2016.
Kocin ya bayyana bacin ransa akan dabi’un ’yan kwallon da ya gayyato inda da yawa daga cikinsu suka ki amsa gayyatarsa na halartar sansanin horar da su a kan lokaci. Kocin wanda tsohon dan kwallon kungiyar Super Eagles ne, ya nanata cewa kada wani ko wasu su ce za su zarge shi idan kungiyar ta kasa hayewa gasar saboda rashin kwakkwaran shirin da kungiyar ta yi kawo yanzu.
Ya kuma koka a kan yadda Hukumar shirya kwallon kafa ta NFF ta ki biyan alawus-alawus na ’yan kwallon kungiyar har na tsawon watanni 9. Ya ce ta yaya ake tsammanin ’yan kwallon za su cigaba da nuna kwazo alhalin ba a biya su wasu hakkokinsu a kan kari ba?
“Abin mamaki ne yadda Hukumar NFF ta biya ’yan kwallon Super Eagles dukkan alawus dinsu, har da wanda suka yi kunnen doki da Burkina Faso a makon jiya amma ta ki biyan na U-23, a duk lokacin da na nemi su biya namu alawus din sai su ce babu kudi”, inji shi.
kungiyar U-23 dai za ta fafata ne a gasar cin kofin Afirka na ’yan kasa da shekara 23 (U-23) da zai gudana a Senegala a tsakanin ranakun 28 ga watan Nuwamba zuwa 12 ga Disamban wannan shekara inda daga ne za a ware kasashen da za su wakilci nahiyar Afirka a gasar Olamfik da za ta gudana a badi a Brazil idan Allah Ya kaimu. Najeriya za ta fafata ne a rukunin B da kasashen Egypt da Mali da kuma Aljeriya.