Wani mutumin birnin New York da ke kasar Amurka ya kafa tarihi bayan da aka auna kabewarsa kwaya daya aka gano ta fi tan guda.
Manomin mai suna Scott Andrusz na garin Williamsbille, ya kai babbar kabewar tasa ce zuwa gonar Great Pumpkin Farm da ke Clarence, New York, inda aka auna ta aka gano ta kai nauyin kilo 1,158.475.
Kabewar ta Andrusz ta karya tarihin kabewa mafi girma da aka taba samu a kasar Amurka mai nauyin kilo 1,146.682 a baya.
Sai dai duk da haka kabewar ba ta karya tarihin da aka kafa a Kundin Tarihi na Duniya ba inda aka samu mai nauyin kilo 1,225.607 da wani mai suna Stefano Cutrupi ya noma a kasar Italiya a bara.
Ta yiwu nan gaba Andrusz ya shiga gasar Travis Gienger na Anoka, a Minnisota, idan ya samu irin kabewar da za ta iya karyar tarihin da Cutrupi ya kafa.
An yi bikin auna kabewa ta Gienger ne a ranar Litinin a wata gasar Auna Nauyin Kabewa ta Duniya da za a gudanar a Kalifoniya ta Amurka.