Sarkin Kano na 14, kuma Halifan darikar Tijjaniyyah na Najeriya, Muhammadu Sanusi II, ya sami ganawa da Shugaban mulkin soja na Jamhuriyar Nijar, Abdulrahmane Tchiani.
An yi ganawar ne a Yamai, babban birnin Nijar din a ranar Laraba.
Wannan ne dai karo na farko da aka ga Shugaban mulkin sojan ya amince ya gana da wata tawaga tun bayan hambarar da gwamnatin Mohammed Bazoum a karshen watan jiya.
Idan za a iya tunawa, Shugaban ya ki amincewa da tawagar da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) da na Tarayyar Afirka (AU) da ma Sakataren Harkokin Wajen Amurka.
Ana ganin Sanusi dai na da kyakkyawar alaka dadaddiya da shugabannin siyasa da kuma masu rike da sarautun gargajiya a kasar.
Bugu da kari, ana ganin matsayinsa na jagora a darikar Tijjaniyya, wacce take da dimbin mambobi a kasar sun taimaka wajen samun damar ganawa da shugaban.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton dai, babu cikakken bayani a kan abin da suka tattauna.